Rubutu da marubuta da ci gaban kasa (2)

Wannan ba wani abu ya nuna mana ba sai gadon gida alala ne ga rago. Ba ta yadda za a kai ga kololuwar ilimi da ci gaba ta amfani da bakon harshe, domin kuwa komai iya nakaltar harshen wasu da aka yi, ba za a taba zama kamar su ba, kuma za a kasance ne […]

Rubutu da marubuta da ci gaban kasa (2)
Rubutu da marubuta da ci gaban kasa (2)

Wannan ba wani abu ya nuna mana ba sai gadon gida alala ne ga rago. Ba ta yadda za a kai ga kololuwar ilimi da ci gaba ta amfani da bakon harshe, domin kuwa komai iya nakaltar harshen wasu da aka yi, ba za a taba zama kamar su ba, kuma za a kasance ne a kullum ana magana da su bakin, ba mutanen cikin gida ba, domin kuwa kashi 7 cikin 10 na mutanenmu ba su san da wannan bakon harshen ba, idan kuwa haka ne, to mu da wa muke magana a rubuce-rubucenmu? Shin marubutan baya haka suka yi? Yaya tasirin wannan abu yake ga ci gabanmu da al’ummarmu da kuma kasarmu da nahiyarmu?
Mu tuna fa su su kansu Turawan mulkin mallaka da suka cusa mana wannan tunani sun san irin ratar da Larabci ya yi wa sauran harsunan duniya kafin su durkusar da shi, su maye gurbinsa da nasu, shi ya sa duk inda suka samu kansu a matsayin masu mulkin mallaka, a Afirka ko Asiya ko Amurka ba su yi wasa da cusa tunaninsu da kuma akidojinsu ga al’ummomin da suka ci karo da su ba. Sun yi haka ne da sani, domin ta haka ne kurum za su iya yin zaman dirshan a cikin harkokin kasashen da suke yi wa sukuwar salla a wancan lokaci.
Shi ya sa tsarin ilimin da suka shigo mana da shi da littattafan da suka tsara da kuma wadanda suka zo da su domin horarwa, suka kasance cikin harshen ’yan mulkin mallakar, a wasu wurare suka matsa sai a yi komai tamkar a Turai, a wasu wuraren kuwa a kaikaice, wasu kuma ba ka iya bambanta su da masu mulkarsu ta kowace irin fuska. Dubi Amurkawa ka kwatanta su da mutanen Indiya ko Pakistan da kuma bakaken fatar Afirka, musamman a tsakanin inda Faransa ta yi turke da kuma inda Birtaniya ta kafa tata lemar. Ma’ana, wannan rarrabuwar ita ce ta taimaka wajen gane illar mulkin mallaka da kuma yadda aka rarraba kawuna domin a ji dadin mulki. Bisa wannan tafarki ne Leopord Senghor na Senegal ke nuna bakin cikinsa game da irin ilimin da ya samu ta hanyar Turawan Faransa, yana cewa:  “A lokacin da nake fafutikar karatu a gida da waje, ’yan uwana da na bari a gida ba su yi boko ba, sun kasance ’yan kasa nagari, ni kuwa a kullum da na bar firamare na shiga sakandare, na wuce zuwa jami’a, sai kara hannun riga na yi da al’ummata da kuma kasata.” Ya kara da cewa “A daidai lokacin da nake karatu, sai na ga kullum ina kara sanin tarihi da yanayin kasashen Turai, ina kuma kara jahilcewa game da tarihin al’ummata da kuma kasata.”  Ya sake nuni da cewa: “A lokacin da na dawo gida daga Faransa, bayan kai makurar ilimi, sai na ga na kasance bako cikin jama’ata, tsararrakina da na bari ba su yi karatu ba, suka kasance malamaina.”
A lura da kyau a nan ba Leopord Senghor kadai wannan tarmahaha ta yi wa katutu ba, haka ya kasance dangane da yawancin marubuta da shugabanni a Nahiyar Afirka, musamman wadanda suka kasance karkashin mulkin Faransa.
A bangare daya kuwa, wadanda suka zauna cikin inuwar mulkin Birtaniya ba haka abin ya kasance ba, ga wasu, kamar yadda Mista East ya bayyana game da Abubakar Imam a kasar Hausa, a matsayinsa na marubuci, ya ce: “Abubakar Imam ya kasance daya daga cikin ’yan kalilan daga mutanen Afirka da ya kasance duk da cewa ya samu iliminsa ta hanyar horarwa cikin Ingilshi da littattafan Ingilishi, daga kuma Turawan Ingilishi, bai yi watsi da harshensa ba, domin kuwa yana bayyanar da tunaninsa cikin harshen nasa, ba cikin Ingilishi ba kamar yadda saura ke yi.” Me ya bambanta Senghor da Imam? Ba wani abu da ya bambanta su ba sai ganin cewa shi Abubkar Imam bai yarda Ingilishi ya kasance masa harshen tunani ba, ba ma Ingilishi kadai ba, kusan duk wani harshe da ya ci karo da shi a lokacin da yake nadar ilimi da ya gina masa rayuwa, bai yarda ya yi masa tarnaki ba. Shi kuwa Senghor ya tashi ne cikin wani tsari da ya fifita tunanin Faranshi bisa na bakar fata, haka al’adu da addini da kuma tsarin ilimin baki daya. Senghor bai samu damar bambance barcin makaho ba ko kuma duma daga kabewa ba, ba don komai ba kuwa sai saboda irin yadda aka rene su tun daga gida, har waje.
Abubakar Imam ya samu fandarewa ne ganin cewa ya sadu da ilimin addinin Musulunci mai zurfi ko kafin ya hadu da Bature da walankeluwar da ya zo da ita, saboda haka bai yarda wani makiri ya yi masa wayon wanikiki ba, tun yana karami. Ko da ya shiga dakin ajiyar littatafai na makarantar Midil a Katsina domin ya yi nazarin da zai shiga gasar littattafai da aka shirya a 1933, bai yarda ya yi amfani da duk abin da ya ci karo da shi ba, sai da ya karanta, ya auna da abin da addinin Musulunci da kuma tadojin Hausawa na kwarai suka aminta da su, sa’annan ya kattaba shi a cikin nasa aikin, kuma bai taba yarda da tasirin bakin al’adu ko addinai sun ja masa akala ba.
Haka su Tafawa balewa da Ahmadu Bello da Aminu Kano da Sa’adu Zungur da wasu da dama, kuma wannan shi ya haifar da akidar nan ta NEPU da neman canji a wannan yanki namu da kuma gina ayyukan adabi da suke tasiri har yanzu, sama da shekara 80 da samuwarsu. Ba irin yanzu ba da an yi rubutun aikin adabi, bayan watanni ko ’yan shekaru, sai ka ji tsit kamar an yi ruwa an dauke.
 Za mu ci gaba