Rubutu da marubuta da ci gaban kasa (3)
Mu koma ga gagarabadan adabin Hausa, wato Abubakar Imam. A cikin ayyukan da Abubakar Imam ya yi na adabi ba wanda ya zauna ya shirya a cikin ransa da nufin ya nishadantar ko ya burge ko kuma dai a san da shi a cikin harkar rubutu ko kuma rayar da ilimi kai-tsaye ba. Bai yi […]
Mu koma ga gagarabadan adabin Hausa, wato Abubakar Imam. A cikin ayyukan da Abubakar Imam ya yi na adabi ba wanda ya zauna ya shirya a cikin ransa da nufin ya nishadantar ko ya burge ko kuma dai a san da shi a cikin harkar rubutu ko kuma rayar da ilimi kai-tsaye ba. Bai yi haka a lokacin rubuta Ruwan Bagaja ba, duk da cewa a lokacin da ya yi rubutun yana da shekara 21 a doron kasa. Ko da ya shiga dakin ajiyar littattafai na makarantarsu domin ya samu samfuri na irin yadda zai tsara labarin nasa, ya kuma ci karo da littafin The Water Of Cure na ’yan uwa Grimms daga kasar Jamus, ba haka nan ya bi shi ya kwashe ko ya wanke komai da ke ciki ba kamar yadda labarin yake a kasar Jamus, tun asalinsa, sai da ya bi ya yi masa kwaskwarima ya debe al’adun Jamusawa da ya san ba za su amfanar da rayuwar Hausawa ba, sa’annan ya shigar da na Hausa. Ya kuma bi ya cire addinin Kiristanci da ya ci karo da shi, ya shigo da Musulunci.
Wani zai ce to sai adabin da bai da alaka da al’adun Hausawa da addinin Musulunci ya yi wa irin wannan wanka? Ko alama! Ko da ya shiga cikin rumbun littafin Alfu Lailah ya debo hikayar Abdussamad da ’yan uwansa da ke ciki, ita kuma ya kwashi wani gefe da ya dace da tunanin Malam Bahaushe ya jefa a cikin Ruwan Bagaja, ya yi watsi da tadar Larabawa da ya san cewa ba ta da wani alfanu ga mai karanta Hausa. A cikin irin wannan fasali ne ya kuma koma cikin gonar adabin baka na Hausawa, inda ya tsamo tatsuniyoyi da labaran Hausa da suka yi tashe a wancan lokaci ya gina zubin littafin.
Idan aka natsu da kyau za a ga cewa ba inda ya fi fiddo da tsarin kyautata wa adabi fili irin yadda ya nemi Malam Zurke da Alhaji Imam daga rayuwa ta yau da kullum. Shi dai Zurke wani mahaukaci ne da aka yi a cikin birnin Katsina, Alhaji Imam kuwa marubucin ne, amma kuma wadannan mutane a zahiri ya same su ne daga littafin Makamatul Hariri, inda Harisu da Abu Zaid suka taka rawa irin ta Zurke da Alhaji Imam, sai dai su Harisu da Abu Zaid dabaru da wayon wanikiki da suka yi a cikin Makama cike suke da al’adun Larabawa, dole ta sa Imam ya mayar da su na Hausawa, cikin ban dariya da sosa rai.
Ba wannan kadai ba, idan kuma muka dubi Magana Jan Ce (1-3) sai mu ga cewa nan Imam ya nuna gwanancewa fiye da a Ruwan Bagaja, ko ba komai a nan ya san da wa yake magana, ya kuma san dalilin yin rubutun da abin da yake son rubutun nasa ya yi ga wadanda aka yi wa rubutun. Tun da farko, nan ba gasa ba ce, an nemi a yi rubutu ne don yara ’yan firamare, domin a samar musu abin karatu da kuma tarbiyya. Nan ma Abubakar Imam sai da ya nemi samfur da zai gina nasa tunanin, amma kamar kullum sai da ya canza wa duk wani tubali da ya tsinto daga wasu wurare masu siffofi ko kuma kamanni, mabambanta, don su dace da yara ’yan kasar Hausa. Ya dubi tsarin Alfu Lailah, na Larabawa, ya gina budewar Magana Jari Ce. Ya kuma yi amfani da littafin The Parrot, na Turawa ya gina batun Aku mai magana. Ya nemo Andersen Fairy Tales na kasar Denmark da Aesop Fables labaran Girkawa da Grimms Fairy Tales na Jamusawa da kuma tatsuniyoyin Hausa domin su kasance masa ’ya’yan da ke tafiya da uwar labarin Magana Jari Ce. Ya yi haka ne cikin tunanin makarantarsa, duk inda ya hadu da maganar barayi sai ya yi huduba kan sata da rashin kyan sata, yana kuma bayyana cewa bai son bayar da labarin barayi, ba don komai ba, sai don gudun kada yara su samu abin kwaikwaya. Haka kuma duk inda ya kawo labarin barayi, to bai barin su yi nasara. Kai ba wannan kadai ba, duk inda aka yi mugun abu sai ya nuna horon da aka yi wa wanda ko wadanda suka yi mugun abin, kamar yadda ya fada a cikin littafin tarihinsa. Ya ce Dokta East, malaminsa na farko a harkar rubuce-rubuce ya koya masa cewa kada ka yarda ka bar mugu ya yi nasara a cikin gina labarinka, domin tasirin barin haka zai iya rusa al’umma. Wannan shi ne ke cikin zuciyar yawancin ayyukan adabin da Abubakar Imam ya gina a cikin Magana Jari Ce. In da ya ji ana maganar itaciyar Yeuw (mai kwankwamai) sai ya mayar da ita itaciyar tsamiya. Gidan Turawa na ginin bene, ba zaure don baki da sa kwat da duk wasu abubuwan jin dadi nà rayuwa, irin na Turawa, canza su yake yi da na Hausawa, bai yarda bakon Malam Bahaushe ya shigo har cikin gida ba, domin masaukin bako ai zaure ne inji Hausawa. Haka abinci da abin sha da abin hawa da sauran makamantansu, ba don komai ba sai don wadanda yake wa rubutun su karu da ilimin da ke ciki da kuma inganta kyawawan al’adu.
Abubakar Imam bai yarda ya bar mugu ya sha ba, bai bar azzalumi ya wuce da zaluncinsa ba, bai kuma bar kunci ya tabbata a cikin rayuwa ba a cikin ayyukansa na adabi. Duk yadda zai yi ya nuna wa yara kyau da rashin kyan abu, shi ya bi ya gina tunanin nasa adabin, wannan kuma shi ya sa, har yau har kwanan gobe ayyukan nasa suke kasancewa kamar yau ne aka yi su duk da cewa sun yi fiye da shekara tamanin da dabbakawa. Darussan da ke ciki har yau suna da tasiri a rayuwar jama’ar yau din ba wa sai na jiyan ba, za su kuma ci gaba da wanzuwa a haka har gobe.
Tambayar da kila wasu ke faman yi har yanzu ina jin ba ta wuce to mu wa muke wa rubutu ba? Kanmu ko gwamnati ko talakawa ko masu ilimi ko kuma madaidaita ilimi ko kuma dai kowa da kowa? Yanzu kuma dabara ta rage ga mai shiga rijiya.
Mun kammala