Rubutu da marubuta suna da muhimmanci sosai – Kabiru Fagge
Aminiya ta zanta da wani fitaccen marubuci kuma dan jarida mai suna Kabiru Yusuf Fagge (Anka) inda ya bayyana yadda ya tsinci kansa a cikin harkar rubuce-rubuce da kuma matsalolin da marubuta suke fuskanta da yadda za a magance su: Mene ne takaitaccen tarihinka? Sunana Kabiru Yusuf Fagge (Anka). An haife ni a Unguwar […]
Aminiya ta zanta da wani fitaccen marubuci kuma dan jarida mai suna Kabiru Yusuf Fagge (Anka) inda ya bayyana yadda ya tsinci kansa a cikin harkar rubuce-rubuce da kuma matsalolin da marubuta suke fuskanta da yadda za a magance su:
Mene ne takaitaccen tarihinka?
Sunana Kabiru Yusuf Fagge (Anka). An haife ni a Unguwar Fagge. Na fara karatun Alkur’ani a makarantun allo da Islamiyya ta Sabilul Rashad da ke Gyadi-Gyadi da Mukhtariyya Islamiyya da ke Unguwar Fagge da kuma Thimarul kur’an (bangaren dare) har na kai ga sauke kur’ani, da karanta sauran littattafan addini. Na fara karatun firamare a Kurna Special Primary School da sakandare a JSS Kurna, sai Jami’ar Bayero inda na samu shaidar Difloma a bangaren aikin jarida (Mass Communication), sannan na samu shaidar Difloma a bangaren kididdiga (Statistics), da kuma Difloma a kimiyyar na’urar Kwamfuta a makarantun: Online Computer da kuma Hands-On Computer Institute inda na karanci (Desktop Publishing and Data Processing and Maintenance), sannan na karanci Film and Telebision Production a Jami’ar Northwest da ke Kano. Na samu kwarewa a fannin sarrafa na’urar kwamfuta musamman a bangaren zane da bugu (design graphics and typing). Na buga littattafai, da jaridu da mujallu masu yawa a kwamfuta, na kuma tsara shafukan mujallu da jaridu da kuma tsara bangon littattafai da yawa. Na yi rubuce-rubuce a jaridu da mujallu kamar haka:
Wakiliya- (mujallar Marubuta) a matsayin Mataimakin Edita. Da Inuwar Marubuta (Mujallar Marubuta) – a matsayin marubuci na musamman, sai kwallon kafa (Mujallar Labarun Wasanni) a matsayin Mataimakin Edita da Muryar ’Yanci (jaridar labaran karamar Hukumar Fagge) a matsayin Edita. Sai Masoya (mujallar labaran rayuwa da soyayya) a matsayin Edita. Da kuma Kakaki (mujallar kare ra’ayin karamar Hukumar Fagge) ita ma a matsayin Edita. Haka na yi rubuce-rubuce da dama a jaridu da mujallu na kasar nan. Kuma na wallafa littattafai da dama.
Yaya aka yi ka tsinci kanksa a harkar rubuce-rubuce?
Tun ina aji hudu a firamare na zama mai iya karance-karancen littattafan Hausa da jaridu, ni da wani abokin karatuna mai suna Abdulhamid wanda asalinsa kwara ne, da shi muke sayo littattafan da jaridu muna karantawa, don haka sai na fara karanta Magana Jari ce a ajinmu, daga nan ne kawai sai na samu kaina a harkar rubuce-rubuce.
Littafai nawa ka rubuta zuwa yanzu?
Na rubuta littattafai da dama, amma wadanda na fitar guda goma sha daya ne bangaren hikaya:
1. karfin Hali
2. Shure-shure
3. Ninkaya
4. Alwashi
5. Bilkisu
6. Firgita Samari
7. Rayya
8. ’Yanmata
9. Kushewar Badi
10. Launin So
11. ’Ya’yanmu
Sai kuma littafan wasan kwaikwayo:
1. Kowa ya yi da kyau
2. Kurman Amo,
Sai kuma littattafan da suka shafi ban-dariya da hikaya:
1. Mu Sha Dariya
2. Kai Ma Ka Dara
3. Abokin Dariya
4. Malamin Ban Dariya
5. A Ba Su Dariya
6. Gidan Dariya
7. Zumbuli Kakan Marowata
Sannan akwai littattafan da suka shafi koyar da yara kanana karatu da rubutu kamar:
1. Standard Dictionary
2. The Boy Who Cried Wolf
3. Alphabet for Kids
4. Mathematics for Kids
5. Successful Drawing Book for Children
Da sauransu sannan na rubuta fina-finan Hausa da dama.
Wane littafi ka fi so a cikin littafanka?
Ina son dukan littattafaina. Dalili kuwa saboda kowanne akwai dalili mai karfi da ya sa na rubuta shi.
Wane marubuci ne kake koyi da shi?
Na san dai na karanta littattafan Bala Anas Babinlata da Abubakar Imam sosai, da kuma littafan su Nazir Adam Salih da Habibu Hudu Darazo da Ibrahim Birniwa da Rahma Abdulmajid da Zuwaira Isah da sauransu.
Ko kana da kira ga marubuta ’yan uwanka?
Ina kira ga marubuta da duk wanda zai yi rubutu ya fara sanin dalili da manufar yin rubutunsa, sannan koda marubuci ya fara yin rubutu, to ya rika yawaita karatu da kuma neman ilimi a kan rubuce-rubuce.
Ko kana da kira zuwa ga gwamnati?
Maganar gaskiya, gwamnatocinmu ba su san darajar rubutu da karatu ba, shi ya sa ba su cika damuwa da al’amuran marubuta ba. Za ka ga suna bibiyar al’amuran masu shirya fina-finai ko mawaka, amma sam ba su damu da marubuta ba.
Yana da kyau gwamnati ta san mene ne rubutu, kuma wane irin taimako littattafai ke yi ga al’umma da marubuta, su rika tallafawa a cikin duk wasu al’amura da suka shafi rubutu da marubuta.
Wane kalubale kuke fuskanta a matsayinku na marubuta?
Marubuta suna fuskantar tarin matsaloli musamman a wannan lokaci, wanda ya sa a dole wadansu suka hakura da harkar rubuce-rubuce, hatta su kansu ’yan kasuwar littafan wadansu sun daina kasuwancin sun sauya sana’a. Ire-iren matsalolin sun hada da: Rashin kudi ko tallafi daga ko’ina da za su yi harkar buga littafan ga al’umma ba su damu da karance-karance ba, kuma gwamnati ba ta damu da harkar marubuta ba, ga satar fasaha ta yadda kowa na iya daukar littafin marubuci ya sarrafa shi yadda ya so a wannan zamani ba tare da izini ko yardar marubuci ba. Wannan satar fasaha ita ta yi mummunar lalata kasuwancin littafin. Ana karanta littafi ko sake bugawa a rika turawa a wayoyi wanda wannan ya sa aka daina sayen littafina. Kuma kasuwancin littafi yana daya daga cikin babbar illa a harkar littafi, saboda ’yan kasuwar na sayar da littafin su hana kudin, ko ma su ki sayarwa. Sannan ga rashin fadada harkar kasuwancin da sauransu
Yaya za a yi a magance wadannan matsaloli?
A rika samun tallafi da gasa da sauransu. Kuma a rika wayar da kai da cusa akidar karatu ga al’umma musamman yara da matasa. Sannan a bi hanyoyin kiyaye hakkokin rubutu kamar copyright da sauransu, kuma a fadada harkar kasuwanci da kuma yin adalci daga ’yan kasuwa.