Rubutu don yara!
A makwannin da suka wuce mun yi bayani ne kan dalilan da suka sa ake yin rubutu da irin muhimmancin rubutu ga al’umma. Ganin irin yadda aka yi ta aiko da sako kan cewa ko akwai bambanci tsakanin rubutu don manya da kuma rubutu don yara, ya sa zan karkata linzami don mu kalli […]
A makwannin da suka wuce mun yi bayani ne kan dalilan da suka sa ake yin rubutu da irin muhimmancin rubutu ga al’umma. Ganin irin yadda aka yi ta aiko da sako kan cewa ko akwai bambanci tsakanin rubutu don manya da kuma rubutu don yara, ya sa zan karkata linzami don mu kalli wannan fage shi ma.
Shi wannan fage na gina labarai domin yara dadaddiyar al’ada ce a doron kasa, kuma ita ce hanya mafi sauki wajen kokarin cusa wa yara da matasa halaye nagari don su kasance masu kula da inganta rayuwar al’ummar da za su wanzu a cikinta. Shi ya sanya a can baya a fadojin manyan sarakuna a sassan duniya ake da masana ko manyan masu iya ba da ko rubuta labarai domin nusar da al’umma. Yawancin irin wadannan labarai don yara ana tsara gina su da wasu manufofi a zukatan ko dai hukuma ko kuma wadanda sana’ar tasu ke nan. Akwai ire-iren wadannan ayyuka a nahiyoyin Turai da Asiya, a Afirka kuwa yawanci da yake ba a da al’adar rubutu irin ta zamani, sai da baki suka shigo, hanyar gargijiya ita aka fi ba muhimmanci, duk da cewa ko a Turai da Asiyar ma ana gwamawa tsakanin gargajiya da zamani.
Marubuta tatsuniyoyi da hikayoyi da labarai irin na su Aesop Fables da Kalilah Wa Dimna da Makamatul Haririh da Andersen Fairy Tales da Grimms Fairy Tales da Tales From Shakespeare da wasu da dama irinsu, sun samar da su ne da tunanin yara ko domin yara da matasa, sai dai in manya sun karanta, ba laifi, domin karuwar kowa da kowa ce. Ke nan idan mutum ya nazarci wadannan ayyuka zai iya gane cewa labarai irin wadannan suna zuwa da jigogi mabambanta, sa’annan akwai sakonnin da ake kebewa don isarwa ga mai karatu. Mu dubi misalin Labaran Aesop, kowane da darasi a karshe domin a fahimci inda aka nufa. Haka sauran an gina su ne bisa tsarin tatsuniya da hikaya domin yara su yi saurin tsinkaya, misali Andersen Fairy Tales tatsuniyoyin kasar Denmark ne aka tace, haka kuma Grimms Fairy Tales na Jamus ne aka tattara, su kuwa Kalilah Wa Dimnah da Makama labarai da hikayoyi ne na Asiya da kasashen Larabawa, domin yara.
Ke nan za mu iya cewa tun farkon fari, adabin labari na Hausawa da aka assasa, an yi haka ne da sani da kuma tunanin yara kamar yadda masu rubutun suka yi tun da farko, musamman ganin cewa sun samu tasirin yin haka daga ko dai tatsuniyoyi da labaran Hausa ko da ilimin rubutu ya shigo musu, sun kwaikwayi na Turawa da Larabawa da suka ci karo da su. Wannan fasali shi ne ya samar da littafin Ruwan Bagaja da Shaihu Umar da Gandoki, wadanda tun daga budewarsu za a ga sun zo da fasalin bayar da labarai irin na Hausawa. Misali, Ruwan Bagaja, labari ne cikin labari, yadda Koje Sarkin Labari ke samar da bayar da labarai irin yadda Hausawa suka saba ne, ko da Koje kuma ya zo jin labarin Alhaji Imam, bisa wannan tsari aka samar da shi, “Kunnenka Nawa? Koje ya ce Kunnena biyu…” Haka in aka dubi Gandoki, yara ne ya tara yana ba su labarin rayuwarsa da yake-yaken da ya yi. Shi ma Shaihu Umar, dalibansa a makarantar Allo yake ba labarin abin da ya faru da shi har ya zama Shaihun Malami. Irin haka ya samar da Magana Jari Ce da karamin Sani kukumi Ne. Wadansu za su iya cewa dole sai an yi aro kafin a tsara irin wadannan labaran? Ba laifi ba ne yin haka, domin yana kara wa aikin adabi armashi da inganci.
Bari mu dubi fasalin yadda aka samar da Magana Jari Ce don ya kara mana haske. An shirya littattafan Magana Jari Ce don su zama abin karantawa a makarantun Arewacin Najeriya, a maimakon Aljaman Yara da Littafin Koyarwa Na Karatu Da Rubutu da ake da su a farkon shekarun 1920 zuwa 1930, wadanda ba su yi kama da littattafan adabi ba. Haka kuma an tsara littattafan Magana Jari Ce ta yadda za su sha bamban da littattafan Hausawa Da Makwabtansu da Labaru Na Da Da Na Yanzu da Al’amurran Duniya Da Na Mutane, wadanda suke da alaka da tarihi ko gaskiyar aukuwar al’amurra.
Rahoton Hukumar Fassara na 1936 ya bayyana a fili matakan da aka bi aka samar da littattafan Magana Jari Ce, ya ce an yi amfani da wasu labarai daga littattafan labarai da tatsuniyoyin sassan duniya daban-daban, aka sake rubuta su ta la’akari da tunanin mai karatu dan Afirka. Ke nan ba laifi ba ne mutum ya nakalci wasu ayyuka na baki ko ’yan gida wajen gina labarai don yara. Abin da ake bukata shi ne darussan su kasance domin yaran da kuma manufar isar da wani sako na musamman.
Me ake bukata a yi a cikin ayyukan adabi domin yara? A tabbata an kulla labarin ilimi da sa nishadi a wuri daya.
Misalin da za mu iya kawowa a nan shi ne na littafin karamin Sani kukumi Ne. Wannan littafi ya wanzu ne daga fahimtar da aka yi ta cewa litattafan Magana Jari Ce sun yi wa daliban da aka shirya su domin su tsauri. Tun da farko dai an tsara Magana Jari Ce domin ta kashe kishirwar da daliban Elemantare ke fama da ita na rashin abin karatu, duk da cewa an samar da abin karantawar, ganin cewa ya fi karfin masu karatun, dole ta sa aka shiga neman mafita. R. M. East wanda shi ne Shugaban Hukumar Talifi a lokacin, wadda ta samar da littattafan ya bayyana yadda aka tsara littafin a 1938, ya ce da Abubakar Imam, wanda shi ne asasi; akwai wani rubutu da za mu yi mai muhimmanci wanda zai dauke mu awa biyu ko uku a rana muna yi. Tun da ba za ka iya zuwa Zariya ba, to zan yi kokari in iske ka Katsina, mu yi aikin tare.
Za mu ci gaba