Rudani kan hana Keke NAPEP aiki a Abuja
A ranar Talatar makon jiya ne Hukumar Birnin Tarayya Abuja ta hana ayyukan masu haya da Keke NAPEP a cikin gwaryar birnin. Mutane da dama sun yi ta tafiya mai nisa a kafa kafin su kai wuraren aikinsu dalilin wannan doka ta haramta zirga-zirgar Keke NAPEP. Da dama daga cikin masu wannan sana’a ta jigila da […]
A ranar Talatar makon jiya ne Hukumar Birnin Tarayya Abuja ta hana ayyukan masu haya da Keke NAPEP a cikin gwaryar birnin. Mutane da dama sun yi ta tafiya mai nisa a kafa kafin su kai wuraren aikinsu dalilin wannan doka ta haramta zirga-zirgar Keke NAPEP. Da dama daga cikin masu wannan sana’a ta jigila da KEKE sun samu labarin fara aikin wannan doka ce a wannan safiya ta Talata bayan da suka fito da zimmar aiki kamar kullum kafin daga bisani su ga ’yan sanda suna bin su suna kamawa tare da kwace musu baburansu.
Hukumar Tabbatar da Doka da Oda ta Birnin Tarayyar da hadakar jami’an tsaro suka gabatar da aikin tabbatar da kawar da masu Keke NAPEP daga kan manyan hanyoyin birnin Abuja. Shugaban Hukumar Kwamared Ikharo Attah, wanda ya jagoranci wannan aiki ya tabbatar da cewa za su ci gaba da aiki ka’in-da-na’in har sai sun tabbatar da sun tsabtace birnin daga cinkoson ababen hawa da yake fuskanta a yanzu.
Wannan hukuma ta tsabtace birnin Abuja, Ministan Abuja Mohammed Musa Bello ne ya kafa ta wata biyu da suka gabata daga hadakar ma’aikatan ma’aikatu daban-daban. Ayyukan da ya dora mata sun hada da kawar da masu tallace-tallace daga kan titunan birnin da kuma tabbatar da rage cinkoson ababen hawa a birnin Abuja.
A nasa bangare Shugaban Kwamitin Attah cewa ya yi wannan doka ba tana nufin ta ci zarafin masu wannan sana’a ta tuka Keke NAPEP ba ne, amma dokar tana kan kudirin dokar Birnin Tarayya wanda ya fayyace cewa ya kamata a tsabtace tare da inganta hanyoyin sufuri a fadin birnin. Ya ci gaba da cewa umarnin Ministan yana kan inganta rayuwa da kuma lafiyar su kansu masu Keken da kuma fasinjojinsu ta hanayar hana su hawa kan manyan titunan Abuja.
Attah ya ci gaba da cewa wannan doka ba za ta taba samun nasara ba in dai masu ruwa-da-tsaki kan tabbatar da doka da oda ba su hada karfi da karfe wuri guda ba. Ya ce “Abin da Minista yake son su yi shi ne su koma wuraren da doka ta amince musu su yi jigila su ci gaba da ayyukansu. Ba za mu lamunce mu gansu suna ta yawo a ko’ina a cikin Abuja ba, musamman a kan manyan tituna. Sannan yanzu an tanadar da manyan motoci da za su ci gaba da daukar jama’a.”
Muna goyon bayan wannan doka ta Birnin Tarayya da ta hana ayyukan masu Keke NAPEP ganin cewa hakan wani yunkuri ne na rage aukuwar haddura a fadin birnin wanda ganganci da hawa manyan titunan da masu Keken ke yi ke haddasawa, musamman in sun hadu da manyan motoci wadanda iskarsu kadai ta isa ta sanya Keken ya saki hanya. Haka kuma muna maraba da takaita ayyukan masu Keke a cikin unguwanni kawai.
Rudanin da ake bazawa sakamakon wannan doka wacce aka jima da yin ta amma suke karya ta ta hanyar fara bazuwa a kan manyan titunan Abuja suna daukar fasinja ba ya da tushe. Haka kuma kawar da kan da jami’an BIO da jami’an FRSC na kare hadura suka yi a baya shi ya sanya jama’a suke ganin dokar kamar sabuwa ce.
Sai dai ya kamata a ce kafin a sake jaddada wannan doka a makon jiya a sanar da masu Keken da kuma fasinjoji cewa dokar za a farfado da ita. Da a ce an yi haka da ba a sanya jama’a da dama tafiyar kafa ba, tare da haddasa asara ga masu Keken. Haka da a ce jami’an FRSC sun yi aikinsu na hanyar wayar da kan masu tuka Keken da gangancinsu ya ragu a kan manyan titunan. Don haka in ana son a farfado da harkar sufuri a Birnin Tarayya ya kamata gwamnati ta farfado da Kamfanin Manyan Motoci na Abuja Leason Company wanda tsohon Ministan Birnin Tarayya, Malam Nasir El-Rufa’i ya samar a lokacinsa wanda ya samar da motoci masu yawo a kan manyan titunan birnin.