Rudanin raurawar rabon rawunna (1)
Mai martaba Masanin Sisi-da-sisi Hukumar Zakka da hubusi Raba masarauta ake bin bahasi Lalitarka aka ce ba ko asi Lamarin na da jefa wasi-wasi Wassafa laifuka a tafi A kai ta laluben laifi Kai ka ba da kafa marar rufi Aka wangale maka shafi-shafi Har da bin kwakkwafi Mun dai ga Majigin […]
Mai martaba Masanin Sisi-da-sisi
Hukumar Zakka da hubusi
Raba masarauta ake bin bahasi
Lalitarka aka ce ba ko asi
Lamarin na da jefa wasi-wasi
Wassafa laifuka a tafi
A kai ta laluben laifi
Kai ka ba da kafa marar rufi
Aka wangale maka shafi-shafi
Har da bin kwakkwafi
Mun dai ga Majigin makafi
Bugun Shago a kai wa Maikarfi
Wai tagwaye sun yi kofi
Ka da dai a fada rafi
Masunta sun ce ruwan da zurfi
Babban mutum yai jaye-jaye
Rikon igiya na neman yai kaye
Akai ta yaye-yaye
A hankalta ’ya’ya da iyaye
Yau fa gari ya waye
Kai ne wane
Ko dan wane ne
Idan ka shiga bone
Ba ruwan kowa balle ai aune
Ka tsaya tsaf ka gane
Rudanin raurawar rabon rawunna
Rabe-raben kahonni tamfar raguna
Karaga ce da ka zauna
Daga bara zuwa bana
Kai ta taratsin magana
Fadin kasa
Aka karkasa
Mutane na ta busa
Wasu sun karke da sa-in-sa
Ka-ce-na-ce da kulla dasisa
’Yan kore na kalaman kafa kusa
Jagaliya ce ta siyasa
Doka ta malkwasa
Laifuka aka fallasa
Kasurar rigima wasa-wasa
Masu rawunna kadahan-kadaran
Ban da katsalandan
A bari sai an je Lantsandan
A haifar da matsaloli daban-daban
Rawa kan sauya da juyin wani kidan
Sai a rungumin juyin zamani
A bi tarbiyyar iyaye da kakanni
A rinka aiki da sani
A yasar da karambani
A bar yi wa juna gani-gani
Aiki da hankali
Amawalin Malam Mawali
Kasar da babu haraji da jagali
Ba a daukar kudi ai shagali
A bar takaddamar zare kansakali
Hawan dare sirdin akawali
Tufafi na ta kyalkyali
Kayan ado na walwali
Fadin kasa an yi fasali
A dai yi ginin kakkarfan tubali
Sunkurun siyasa na tafarfasa
Kisisinar kissa
Fafatawar samun fursa
In bodari zai karkare tusa
Kowa sai ya gurgusa
Birnin Dabo ba a dabo
Magabta sun lababo
Kulla-kullarsu a hanci na habo
Sun yi wa mahukunta tabo
Don neman sisi da kwabo
Masarautar Kare-kare
’Yan gari ne ba bare
Ko bakon Ba’are
Sai a kiyayi sare-sare
Komai an karkare
Rawanin-nono
Kawanyar bonono
Ana ta kwankwadar fura da nono
Ayyuka tuni an auno
Garma aka ce allura ta tono
Kasar Gayya-gayya
Su ma sun daura aniyya
Bayan tambura an yi jiniya
Inya-inya
Kamar kukan jinjiniya
Birnin Bin-cici
Dan marigayi mai adalci
Nadi akwai wa dan mutunci
Rike sandar yi wa jama’a sassauci
Kar a bari kowa ya shiga kunci
Mahukunta ai ta hukunci
Talakawa ka da ai butulci
A yasar da tumasanci
Don yawansa na sa kaskanci
Masu mulki a kiyayi zalunci
Kaftun kofaton kotu
Kararaki ne rututu
Baje batutuwan bututu
Koken masarautu
A daddale karatun rubutu
Indiyawan Maharaja
Raurawar rangajin Raja
Juyin akalar ragamar ja-in-ja
Tungar dagar mulki an ja
Batutuwa ne baja-baja
A Rasha an yi Sarki Za
Zamaninsa shi ak karzaza
Yai shuhurar kazaza
Mazaje sun yi bugun kiraza
Ahalinsa sun shude ga banza
Birtaniyawa
Har yau suna tattakawa
Sarauniyarsu na da kawa
Lamarinta da ban shawa
Ta rike al’umarta kowa-da-kowa
Can tsakiyar Gabashi kuwa
Larurar lamuran Larabawa
Sarakunansu na tagazawa
Adawar siyasa na angazawa
Damon-kurdiyya na dada kutsawa
Mun dai ga daba
A dambarwar gada-gadar Abba
Yamutsin gundumin gudumar gaba
A hankalta ’ya’yan Inna da Baba
Kowa sai ya duba
***************
Doron damon-kurar-diya
Doron damon kurardiyar kurdiya karon farko da Gwamnatin Baban-burin-huriyya ta bullo da shi a watan Yawon-nunin-wuni, sabon biki ne a jerin ranakun bukukuwan Haurobiyawa, tun bayan dawowa tafarkin Dama-damar-kurda-kurdar siyasar damon-kurar-diya a shekara ta alif sili da muuniyar kasa da ta kasa da ta kasa. An kuma yi wannan namijin kokari ne don tunawa da birkitattar siyasar Haurobiya da ta yamutse zamanin mulkin Baraden bindiga, inda Malam Abiyo-Bala ya lamushe zabi-sonka aka soke, har ta gai ga ba a rantsar da shi a matsayin Shugaban Kasar Haurobiya ba, illa ma dai dauri da ya sha, har rai ya yi halinsa.
Fatanmu dai, wannan lamari ya kasance masalaha ce ga al’ummar kasar nan, sannan yadda ake ganin wadansu sun kwashi garabasar damon-kurar-diya, lallai akwai bukatar kowane yanki na kasar nan a dan jinko musu nasu kason. Bisa wannan dalili ne, nake ganin akwai bukatar ALARAMMAN ALMAJIRAN AREWATAWA da ’ya’yansa kolo da titiribiri da gardin garada a jinko musu nasu ROMON RAGON ROMAWA, ta yadda za su tsahirta da gararamba a kan tituna suna DANDAZON LALUBEN DAN KANZO, da zarar an aiwatar da wannan tsari, har ta kai ga wadannan rukuni na jama’a, sun tsinci kurungunsa a farfajiyar MAKEKIYAR MAKARANTAR MAMA ko a BABBAR BUKKAR BABAN-BURIN-HURIYYA, sai mu ce lallai sun kwashi romon ragon Romawan damon-kurar-diyya.
Kodayake dai ga manyan mutane masu rawunna da kambin gadon rikon ragamar jama’a da ke fama da kwaramniyar Gwamna gwarangwam, musamman a birnin Dabo, inda ba a dabo, Jihar Tumbin-giwa da Jihar Filfilon-toto, inda aka falle fila-filan bangon bangazar buga-bugar bugun bareman bare da nufin a ware. Shin ko su ma dai difara wa al’ummarsu aka yi romon ragon Romawa rurrumarawar rangajin ragargazar damo-da-kura-da-diya. Fatanmu dai ka da a daidaita al’umma. Sai dai mun jiwo cewa can a birnin Shehu Mujadaddi, Gwamna gwarangwam Tumbin-walawalar walle-wallen wulwulawar wulli na yunkurin karin la’adar kadagon kwadagon manyan mutane masu rawunna. Ta yiwu suma sun sharandabi shawarmar siyasa.
Haurobiyawa a sha ruguntsimin biki Fararat far-far a titi firirit!