Rudanin soyayya: Jim Iyke ya rabu da Nadia

Daga dukkan alamu, wutar soyayyar nan da ta yi ta ruruwa tsakanin shahararren dan fim din Najeriya, Jim Iyke da kyakkyawar ’yar fim din kasar Ghana, Nadia Buari ta mutu, musamman a sakamakon labarun da ke gama gari, cewa dan fim din ya rabu da masoyiyar tasa, wacce a can baya aka samu tabbacin cewa […]

Rudanin soyayya: Jim Iyke ya rabu da Nadia

Daga dukkan alamu, wutar soyayyar nan da ta yi ta ruruwa tsakanin shahararren dan fim din Najeriya, Jim Iyke da kyakkyawar ’yar fim din kasar Ghana, Nadia Buari ta mutu, musamman a sakamakon labarun da ke gama gari, cewa dan fim din ya rabu da masoyiyar tasa, wacce a can baya aka samu tabbacin cewa sun gama shirya yin aure.

Kodayake a kwanakin baya an samu wani abin kwarmato da ya shafi shi Jim Iyke, inda wata budurwarsa mai suna Nancy ta yi ikirarin cewa tana dauke da cikin da ya yi mata ba tare da aure ba. Ita dai Nancy, ‘yar wani hamshakin attajiri ce a Legas. Binciken Aminiya ya tabbatar da cewa, duk da wannan abin terere, ita Nadia ta tsaya kai da fata cewa sai sun yi aure da Jim.
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, kafar watsa labarai ta intanet, OluFamous.Com ce ta aika wa shi Jim Iyke sako, tana tambayarsa dalilin da ya sanya zai auri ’yar fim din Ghana, Nadia Buari, inda shi kuma nan da nan ya aika da bayanin da ke tabbatar da cewa lallai soyayya tsakaninsa da Nadia ta yi tsami; har ma yake nuna sun rabu da juna.
Haka kuma, an samu tabbacin cewa, tun kafin shi Jim ya fitar da bayanin rabuwarsa da ita, tuni Nadia ta goge duk wani hotonsa da ke jikin shafinta na Instagram. Daga bisani ne kuma shi ma Jim din ya fitar da bayanin da ke cewa: “Ni a yanzu ba aure ne a gabana ba.” Batun da ke kara tabbatar da cewa lallai dan wasan ya rabu da tsohuwar masoyiyar tasa.
Abin da har yanzu ba a tabbatar ba shi ne, dalilin da ya sanya masoyan biyu suka farrake da juna. Wasu na ganin cewa babban dalili dai shi ne, labarin tereren cikin Nancy ne ya kara dagula soyayyar tasu. Koma dai me ke nan, soyayya tsakanin Nadia da Jim ta samu nakasu, wani gyara sai dai abin da gaba ta haifar.