Rufa’i Chanchangi ya raba motoci 20 da babura 50 ga mutanen mazabarsa
A ranar Asabar da ta gabata ne dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Alhaji Rufa’i Ahamdu Chanchangi na Jam’iyyar APC ya rabar da motoci 20 da babura 50 da kekunan dinki 50 ga jama’ar mazabarsa maza da mata.Da yake jawabi a wajen bikin Alhaji Rufa’i Chanchangi ya ce, ya raba […]
A ranar Asabar da ta gabata ne dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Alhaji Rufa’i Ahamdu Chanchangi na Jam’iyyar APC ya rabar da motoci 20 da babura 50 da kekunan dinki 50 ga jama’ar mazabarsa maza da mata.
Da yake jawabi a wajen bikin Alhaji Rufa’i Chanchangi ya ce, ya raba motoci da baburan ne domin taimaka wa jama’arsa su samu saukin rayuwa.
dan majalisar ya ba da tallafin ne a gidansa da ke Titin Sakkwato a garin Kaduna.
Rufa’i Chanchangi ya ce, duk da mutum ba zai iya yi wa kowa abin da yake so ba, amma dai jama’a da dama za su amfana daga dan abin da ya ware don bayar da wannan tallafi ga wadanda suka dace.
Daga nan sai ya yi kira ga wadanda suka amfana da tallafin, su kula da abin da aka ba su ta yadda zai amfane su da sauran al’ummar da ke tare da su.
Rufa’i ya kuma bayar da mota kirar Golf ga ma’aikatan da ke kula da makabartar da ke kan titin bashama, Tudun Wada, Kaduna. Haka kuma shi ma Shugaban kungiyar Guragu na Kaduna ya samu mota.
daya daga cikin wadanda suka amfana da tallafin, Shugaban Matasan Badiko, Muhammad Sani ya nuna matukar godiyarsa da jin dadi bisa wannan tallafi.