Rufe bankuna a garin Saminaka ya jefa jama’ar yankin a cikin mawuyacin hali
A halin yanzu al’ummar da ke karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna da musamman na garin Saminka hekwatar karamar hukumar da makwabtansu sun shiga cikin mawuyacin hali, sakamakon rufe bankunan First Bank da Keystone da Ecobank da ke Saminaka, bayan da ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, suka kai wa […]
A halin yanzu al’ummar da ke karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna da musamman na garin Saminka hekwatar karamar hukumar da makwabtansu sun shiga cikin mawuyacin hali, sakamakon rufe bankunan First Bank da Keystone da Ecobank da ke Saminaka, bayan da ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, suka kai wa bankunan hari a makon jiya.
Maharan sun halaka soja daya da ’yan sanda guda biyu tare da fasa bankunan Keystone da Ecobank amma ba su samu nasarar fasa bankin First Bank ba.
Binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano ma’aikata da ’yan kasuwa sun shiga cikin mawuyacin hali sakamakon rufe bankunan ta yadda yanzu sai ma’aikatan gwamnati sun tafi garuruwan Jos ko Zariya ko Kafanchan kafin su cire albashinsu a bankunan.
Wani ma’aikacin gwamnati Malam Yakubu Haruna ya ce a gaskiya ma’aikata babu abin da za su ce kan al’amarin, sai dai mu yi addu’ar Allah Ya warware wannan matsala.
Ya ce yanzu idan aka tura wa mutum albashi a banki, dole sai dai ya tafi Jos ko Kafanchan kafin ya samu. “Wannan ba karamin hadari ba ne domin idan aka samu bat gari zasu iya tare ma’aikata a kan hanya su kwace albashin da suka karbo,” inji shi. Ya yi kira ga gwamnati ta samar wa bankunan yankin karin
Wani ma’aikaci Malam Suleiman Rufa’i ya ce a yanzu suna cikin mawuyancin hali, sakamakon rufe bankunan, inda y a yi kira ga bankunan da gwamnati su dubi al’amarin domin magance wannan matsala. Shugaban dillalan hatsi na Kasuwar Saminaka Alhaji Bature Inuwa ya ce sakamakon rufe bankunan yankin yanzu farashin kayayyakin amfanin gona ya karye a Kasuwar Saminaka domin yanzu buhun masara ba ya wuce Naira 3, 500.
Ya ce rufe bankunan ya hana ’yan kasuwa baki zuwa yankin saboda babu yadda za su yi su saka kudinsu su zo su cire a nan.
Ya yi kira ga gwamnati da hukumomin bankunan su magance matsalar ta rufe bankunan, domin a yanzu
harkokin kasuwanci sun durkushe saboda wannan al’amari.
Mataimakin shugaban karamar hukumar dan’azumi Gada ya ce karamar hukumar tana kokarin ganin bankunan sun bude sun koma kan ayyukansu don magance wahalhalun da al’ummar yankin da makwabtansu suke ciki.
Wakilinmu ya yi kokarin tuntubar jami’an bankunan amma abin ya ci tura saboda ba sa garin na Saminaka.