Rufe Boda: Muna  sayar da tirelar shinkafa 6 a mako  –  Alhaji Adamu

Kungiyar  Dillalan Shinkafa ta Kasa Reshen Jihar Nasarawa ta yaba wa Gwamnatin Tarraya a kan rufe iyakokin kasar nan da ta yi. Shugaban kungiyar, Alhaji Adamu Ibrahim ne ya sanar da haka a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Lafiya karshen Disambar bara. Ya ce ba shakka tun bayan da aka rufe iyakokin Najeriya […]

Rufe Boda: Muna  sayar da tirelar shinkafa 6 a mako  –  Alhaji Adamu

Wani sashi na kamfanin gyara shinkafa da ke Jihar Nasarawa

Kungiyar  Dillalan Shinkafa ta Kasa Reshen Jihar Nasarawa ta yaba wa Gwamnatin Tarraya a kan rufe iyakokin kasar nan da ta yi.

Shugaban kungiyar, Alhaji Adamu Ibrahim ne ya sanar da haka a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Lafiya karshen Disambar bara.

Ya ce ba shakka tun bayan da aka rufe iyakokin Najeriya da kuma haramta shigowa da shinkafa daga waje, dillalan shinkafa a jihar suka himmatu wajen kara yawan shinkafar da ake samarwa a gida.

Ya ci gaba da cewa, “duk shinkafar da muka gyara a nan Lafiya zaka tarar tana da haske kuma babu duwatsu da sauransu”. Inji shi. Shugaban ya kuma yabawa Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari, dangane da dakatar da shigowa da shinkafa kasar nan inda ya bayyana cewa ba shakka hakan ya daukaka darajar noman shinkafa da samar wa dinbin mutane aikin yi a jihar da kasa baki daya.

Ya ce, “kafin a dakatar da shigowa da shinkafar da wuya mambobinmu a nan garin Lafiya da jiha baki daya suke sayar da tirelar shinkafa guda daya a mako guda amma a yanzu da aka kafa dokar, mukan sayar da tirelar shinkafa 6 a duk mako a nan garin Lafiya kawai.”

Ya kara da cewa a yanzu kungiyarsu ta kuma kafa wasu injinan gyara shinkafa a wasu kauyukan jihar da a da ba su da su da suka hada da Asakiyo da Ashangwa da Ashige da sauransu, inda kuma ya gargadi mambobinsu da cewa su rika tabbatar da cewa duk shinkafar da aka sarrafa a jihar ingantacciya ce kuma mai haske. A karshe, ya bayyana cewa a yanzu suna da kimanin ma’aikata sama da dubu 28 dake aiki a kamfanonin shinkafa daban-daban.