Rufe gidan rediyo ya haifar da cece-ku-ce a Neja

Jama’a da dama na ganin wannan mataki a matsayin take haƙƙin ‘yancin faɗin albarkacin baki.

Rufe gidan rediyo ya haifar da cece-ku-ce a Neja

Ce-ce-ku-ce ya ɓarke a Jihar Neja, bayan da Gwamna Mohammed Umaru Bago, ya bayar da umarnin rufe gidan rediyon Badeggi FM da ke Minna, Babban Birnin Jihar.

Ya kuma umarci ’yan sanda da Kwamishinan Tsaron Cikin Gidan jihar su rufe tashar, tare da soke lasisinta.

Ya kuma bayar da umarnin bincikar mai gidan rediyon, kan zarginsa da tayar da hankalin jama’a da kuma adawa da gwamnati.

“Tashar na yaɗa kalaman tunzuri,” in ji mai magana da yawun gwamnan, Bologi Ibrahim.

“Gwamna ya umarci jami’an tsaro su ɗauki mataki a kan gidan rediyon da kuma mamallakinsa.”

Sai dai shugabannin gidan rediyon sun ƙaryata zargin.

Daraktan harkokin Badeggi FM, Abubakar Shuaib, ya ce an zalunce su ne ba tare da wata hujja ba.

“Abin da ya dace shi ne a kai wa Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC) ƙorafi, tun da ita ce ke sanya idanu kan shirye-shiryenmu kullum.

“Ba za mu taɓa aikata wani abu da zai tayar da zaune tsaye a jihar ba. Aikinmu dai shi ne mu riƙa sa ido kan shugabanni, ba mu da wani buri na cin zarafin kowa,” in ji shi.

Wannan ba shi ne karon farko da ‘yan jarida ke fuskantar matsin lamba a ƙarƙashin mulkin Gwamna Bago ba.

A shekarar 2023, wani ɗan jarida daga tashar Voice of America, Mustapha Nasiru Batsari, ya ce wani Kwamishina ya zage shi tare da ƙoƙarin ƙwace masa na’urar naɗar bayanai a fadar gwamnatin jihar.

A shekarar 2025 ma, Gwamnatin Jihar ta tsare wani ɗan jarida, Yakubu Mustapha Bina, na tsawon sa’o’i, tare da ƙwace wayoyinsa saboda ya wallafa wani rahoto da ya soki gwamnati.

Umarnin da gwamnan ya bayar ya fusata jama’a da ƙungiyoyi masu zaman kansu.

Ƙungiyar Amnesty International ta bayyana matakin a matsayin cin zarafi da rashin bin doka.

“Zargin gidan rediyo da laifin da gwamnati ke yi shi ne ƙoƙarin kauce wa gaskiya. Gwamna ba shi da hurumin rufe tashar bisa doka. Wannan wani yunƙuri ne na murƙushe ’yancin ’yan jarida da danne muryar jama’a,” in ji Amnesty International.

Muhammad Alfa Muhammad, shugaban ƙungiyar Accountability Ambassadors da ke Minna, shi ma ya soki matakin.

“Rufe gidan rediyo ba tare da bin matakan doka ba babban hatsari ne. Idan akwai wata matsala da gidan rediyon, to ya kamata a miƙa ƙorafi ga NBC. Duk wani mataki da ya saɓa da haka zalunci ne,” in ji shi.

Mutane da dama da ƙungiyoyin fararen hula, da ma ’yan jam’iyyar APC da ke goyon bayan gwamnatun sun nuna damuwa matakin.

Wasu na ganin wannan mataki na iya hana sauran ’yan jarida yin aikinsu saboda tsoro.

Yahaya Adam Idrees, wanda aboki ne ga Gwamnan Jihar Neja, ya bayyana ra’ayinsa a shafin Facebook.

“Dokar ƙasa ta Najeriya ta bai wa kowa ’yancin faɗin albarkacin baki. Ya kamata a sake nazarin wannan doka. Hana kafafen watsa labarai aiki ba abin da ya dace ba ne,” in ji shi.

Wasu mutane sun buƙaci a buɗe gidan rediyon na Badeggi FM nan take, tare da kira ga gwamnatin da ta daina amfani da ƙarfi wajen hana kafafen watsa labarai masu zaman kansu yin aikinsu.

Sun ce aikin ’yan jarida muhimmi abun ne a kowace dimokuraɗiyya kuma dole ne a kare shi.