Rufe iyakokin kasar nan ya gurgunta kasuwancinmu na Roba – Alhaji Abubakar Altine
Tsohon Sakatare Janar na Kugiyar Masu Sayar da Robobi a Jihar Sakkwato Alhaji Abubakar Altine ya ce rufe iyakokin kasa da Gwamnatin Tarayya ta yi ya shafi kasuwancinsu, saboda mutanen da ke zuwa daga Jamhuriyar Nijar sun bar zuwa. “Rufe iyakokin kasar nan ya gurgunta kasuwancinmu yanzu harkokin cikin gida kawai muke yi ba masu […]
Tsohon Sakatare Janar na Kugiyar Masu Sayar da Robobi a Jihar Sakkwato Alhaji Abubakar Altine ya ce rufe iyakokin kasa da Gwamnatin Tarayya ta yi ya shafi kasuwancinsu, saboda mutanen da ke zuwa daga Jamhuriyar Nijar sun bar zuwa.
“Rufe iyakokin kasar nan ya gurgunta kasuwancinmu yanzu harkokin cikin gida kawai muke yi ba masu zuwa ko Karamar Hukumar Illela, cinikin da mutum ke yi na Naira miliyan daya yanzu saboda rufe iyaka ya koma Naira dubu 250,” inji shi.
Alhaji Altine ya fadi haka ne a zantawarsa da Aminiya a ranar Asabar da ta gabata, inda ya yi kira ga gwamnati ta duba yiwuwar dage dokar ta kara inganta tsaron kan iyakoki tsawon awa 24 domin kare shigo da abubuwan da ke lahani ga mutanen kasa. “Addininmu da mutanen Nijar duk guda ne muna taimakon juna, makwabatakar nan tun kafin zuwan Turawa take, a bude iyaka duk abin da yake alheri abar shi ya shigo Najeriya,” inji shi.
Da ya juya kan kasuwancinsu na roba, ya ce “Kasuwancin roba koyaushe ana gudanar da shi tsawon shekara sai dai akwai lokacin da ya fi tafiya kamar lokacin kaka da azumi, kuma mutanen jihohin Kebbi da Zamfara sukan zo Sakkwato su saya. Lokacin da muka fi hada-hadar muna iya sauke tirela biyar na roba koyaushe in ka duba zagayen babbar kasuwarmu za ka ga ko’ina mota ce dauke da roba, in lokacin azumi ne abin yakan ninka domin bukatarta ta karu. A wani lokacin muna sauke mota bakwai zuwa takwas kullum, amma in ba wadannan lokuta ba ne ba za mu sauke mota fiye da biyu zuwa uku ba a mako,” inji Altine Mai roba.
Game da batun rance da Bankin Raya Kasa ya bayar na Naira biliyan 100 ga kanana da matsakaitan masana’antu, ya ce rancen bai iso gare su ba domin su ba huldar karbar bashi karami wanda bai iya tallafawa su yi jari ba. Ya ce duk bashin da bai haura Naira dubu 250 zuwa 500 ba ruwansu da shi, domin su masu sana’ar roba ko a junansu suna iya ba dan uwansu bashin da ya fi wanda ake bayarwar, domin sana’arsu ba karama ba ce.
“Ya kamata gwamnati ta taimaka a kafa masana’antun roba domin duniya ta san Najeriya da roba duk jihar da aka samar da kamfaninta zai tsaya. Rashin jari na ci mana tuwo a kwarya Sakkwato na kan gaba wajen sayen roba a Najeriya daga mu sai Borno, idan ka samu mota 100 sun dauko roba a Kano, 65 Jihar Sakkwato za su tafi 35 ne na Borno, in ka tafi Lagas ma cikin motoci 100 da za su dauko roba 45 Sakkwato za su zo, sauran ne za su je Kano. Rashin jari ne matsalarmu muna son gwamnati ta ba mu jari ba sai mai yawa ba.” inji shi.
Ya ce ba su son bashin banki, saboda duk wanda bai yarda da kaddara ba ’yan kasuwar ba su son hulda da shi kuma ba su son ruwa don haram ne a addini. Ya ce akwai bukatar gwamnati ta hanyar cibiyar ’yan kasuwa ko ma’aikatar ciniki su yi shiri su hadu da Bankin CBN a ga yadda za a tallafa musu. Kuma a rika neman shawarar ’yan kasuwa a duk lokacin da za a kawo masana’antu.