Rufe Kamfanin Triumph illa ce ga Kanawa

Rufe Kamfanin Buga Jaridu na Triumph da Gwamnatin Jihar Kano ta aiwatar, danyen hukunci ne, kuma babban abin takaici ne, musamman idan an yi la’akari da kimar gidan Sa’adu Zungur a daukacin fadin Afirka ta Yamma. Sannan dalilan da ake danganta kulle wannan gida mai dimbin tarihi, sun tabbata abin wasa da hankalin al’umma, musamman […]

Rufe Kamfanin Triumph illa ce ga Kanawa
Rufe Kamfanin Triumph illa ce ga Kanawa

Rufe Kamfanin Buga Jaridu na Triumph da Gwamnatin Jihar Kano ta aiwatar, danyen hukunci ne, kuma babban abin takaici ne, musamman idan an yi la’akari da kimar gidan Sa’adu Zungur a daukacin fadin Afirka ta Yamma. Sannan dalilan da ake danganta kulle wannan gida mai dimbin tarihi, sun tabbata abin wasa da hankalin al’umma, musamman jin cewa ana zargin ma’aikatan kamfanin da nuna goyon baya ga tsohuwar jam’iyyar ANPP.
To, kowane dan Najeriya, kundin tsarin mulki ya ba shi damar tofa albarkacin bakinsa da nuna goyon baya ga jam’iyyar siyasar da ta dace da ra’ayinsa, amma ita gwamnati ai ta kowace, da wanda ya zabeta, da wanda ma bai zabeta. Don haka jingina laifin goyon baya da aka yi wa ma’aikatan wannan kamfani, shiriria ce da wasan yara.
Wani dalilin da gwamnati ta bayar na rue wannan kamfani, shi ne almubazzarancin Naira miliyan 11, inda Naira miliyan ara aka salwantar da ita wajen biyan albashin ma’aikata zaunanannu da ’yan wucin gadi (Permanent da casual). Yanzu an ce yawan kudin ya karu duk da cewa babu Triumph, an rufeta, wato kudin sun kai Naira miliyan 15, inda aka yi amfani da kudin wajen sauya wa ma’aikatan kamfanin wuraren aiki. An kai ma’aikatan wasu ma’aikatn gwamnati da wasu hukumomi. Wannan raguwar dabara ta sanya sauran kafafen yada labarai na samun kudi a jikin Gwamnatin Kano da kimarsu ya kai Naira miliyan 80, a kusan kowane wata, kamar yadda wata majiya daga gidan gwamnati ta tabbatar
Wani dalilin kuwa da aka ce shi ya haifar da rufe wannan gida, shi ne, shugaban Hukumar gudanarwar gidan, wanda ya rika nuna ya fi kowa sanin makamar aiki. Don haka ya bayyana cewa ma’aikatan da ya bari a gidan tsawon shekara 25 su ne dai, don haka akwai bukatar sababbin jinni, wadanda za su aiki mai kyau fiye da tsofaffin da kwakwalwarsu ta dakushe.
Babban abin mamaki shi ne, an kulle wannan gidan jarida ne a karkashin jagorancin malamin jami’a masanin aikin jarida da harkokin yada labarai, kuma da a cikin al’ummar Fagge. Ana ganin wannan malamin jami’a ya fi kaunar ‘Triumph’ ta zama wurin bahayar al’umma, maimakon wurin aiki da hada-hadar kasuwanci.
Tarihi dai ya nuna cewa, wnanan Kamfanin an kafa shi ne a karkashin mulkin alhaji Abubakar Rimi, cikin shekarar 1980, inda aka kuduri manufar wayar da al’ummar Jihar Kano (wadda ta hada da Jigawa), musamman wadanda bas u yi karatun boko ba. Don aka aka rika buga musu jariar Alfijir da harufan Larabci, wato Ajami da harshen Hausa. An kuma yi Al-Bishir ta Hausar Boko.
Uwa-uwa ba, wannan gidan jarida ya riwa wallafa jaridun Turanci cikin harshen Ingilishi, wadanda suka hada da Daily Triumph da Sunday da Weekend. A gaskiya babu wani gidan jarida a daukacin Afirka ta Yamma da ya yi wallafe-wallafe a cikin ajami da Turanci da Hausa kamar gidan Sa.adu Zungur.
Bisa la’akari da abubuwan da muka gabatar game da kulle Kamfanin Triumph, ina fatan gwamanti za ta yi la’akari da illar da ta yi wa kanta da al’ummar jiha. Sannan a tuhumi tsohon shugaban Kamfnin ya yi bayanin yadda ya kashe Naira miliyan 50 da aka ba shi, don tafiyar da kamfanin.
Dalilan dai da aka bayar na kulle wannan kamfani ba su da tushe. Sannan ma’aikatan nan da aka ci wa fuska da cewa kwakwalwar su ta dakushe (deadwood), to a sani, Bahaushe ma cewa ya yi, “da tsohuwar zuma ake magani. A yi wa ma’aikata adalci, a fitar dasu daga rudanin siyasa. Lokaci ya yi da gwamnati za ta sake manufa game da wnanan kamfani, ta yadda kimarta da darajarta za ta karu a idon Kanawa, da ma daukacin duniya baki daya.
Umar Hajjajaj Yusufu ya rubuto makalarsa daga Unguwar Fagge D2, Kasuwar gida mai lamba 170 Kano.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya