Rufe kan iyaka ya bunkasa kasuwancin kayan abinci a Tudun Hatsin Gombe – Auwalu Seiko

Wani matashin dan kasuwa mai safarar kayayyakin abinci a Tudun Hatsin garin Gombe Alhaji Auwalu Isiyaku Seiko, ya ce rufe kan iyakar Najeriya da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya sa aka yi ya zama musu alheri domin ya habaka musu cinikayyarsu na kayan abinci. Auwalu Seiko, ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da […]

Rufe kan iyaka ya bunkasa kasuwancin kayan abinci a Tudun Hatsin Gombe – Auwalu Seiko

Alhaji Auwalu Isiyaku Seiko

Wani matashin dan kasuwa mai safarar kayayyakin abinci a Tudun Hatsin garin Gombe Alhaji Auwalu Isiyaku Seiko, ya ce rufe kan iyakar Najeriya da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya sa aka yi ya zama musu alheri domin ya habaka musu cinikayyarsu na kayan abinci.

Auwalu Seiko, ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a Tudun Hatsin inda ya ce kasuwanci ya bunkasa sakamakon rufe kan iyakokin da Shugaba Buhari, ya yi na hana fita da abincin da ake nomawa a cikin gida a lokacin da sabon amfanin gona yake fitowa.

Ya ce yanzu suna sayar da buhun sabuwar masara Naira 6000 zuwa 6,500 ba kamar a baya da suke sayarwa Naira 8000 ba, inda ya ce farashin wake ya fadi zuwa Naira 11,500 ba kamar yadda suke sayarwa a baya ba Naira 19,000 zuwa 21,000 ba.

Dan kasuwar ya ce yanzu haka buhun sabon gero suna sayar da shi Naira 8000 ba Naira 8,500 ba a kwanakin baya, kuma ba komai ya kawo saukin abinci ba yanzu sai rufe kan iyaka aka hana fita da shi da kuma hana shigowa da wani muna sayen namu da aka noma a kasarmu.

Auwalu Seiko, ya ce da a Tudun Hatsi ba sa sayar da shinkafa ’yar gida amma saboda fara noman shinkafa yanzu suna sayar da ita a kan Naira dubu 14, wadda ake kira Jamila kuma wacce take da kyau sosai suna sayar da ita ce Naira 14,500 buhu mai kilo 50.

Farashin gujiya babban buhu Naira 16,500, komai ya yi sauki ne ba kamar  watannin baya ba saboda hana shiga da fita da abincin da aka yi ne ya jawo haka.

Sai ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Gombe ta taimaka musu wajen gyara musu kasuwar hatsin domin akwai inda katangarta ta zube kuma a samar musu da ingantaccen tsaro saboda kare dukiyarsu da ke kasuwar, sannan a samar da tasha ta motar kashe gobara don gudun faruwar mummunar asara a lokacin da aka samu iftila’in gobara duk da ba fatarta ake yi ba.