Rufe kan iyaka ya inganta harkarmu – Masu harkar roba

Masu harkar sharar roba zuwa wani abin amfanin yau da kullum a Najeriya, sun yaba da rufe kan iyaka da Gwamnatin Tarayya ta yi, inda suka ce matakin ya farfado da harkokinsu da kara bunkasa shi. Wasu masu masana’antun roba da Aminiya ta zanta da su da ke yankin masana’antu na garin Suleja da ke […]

Rufe kan iyaka ya inganta harkarmu – Masu harkar roba

Waxansu matasa na yin bokitin roba a xaya daga cikin masana’antun roba na Suleja

Masu harkar sharar roba zuwa wani abin amfanin yau da kullum a Najeriya, sun yaba da rufe kan iyaka da Gwamnatin Tarayya ta yi, inda suka ce matakin ya farfado da harkokinsu da kara bunkasa shi.

Wasu masu masana’antun roba da Aminiya ta zanta da su da ke yankin masana’antu na garin Suleja da ke Jihar Neja, sun ce kayan da suke sarrafawa da suka hada da ledoji da robobi kamar kofi zuwa bokiti, suna samun tagomashi a wajen dillalansu sakamakon yankewar na kasasshen waje.

Malam Nura Muhammad, wani mai masana’antar robar ya ce duk da inganci da karfin da abubuwan da suke sarrafawa, dillalai sun fi fifita yin sautun na waje irin na China da suka ce ana yin fasakaurinsa zuwa Najeriya, da bai kai nasu inganci ba.

“Hakan ya sa kayayyakin da muke yi ba sa tafiya a baya, amma dalilin yankewar na waje a yanzu sai ga shi dillalan sun karkato wajenmu suna ba da sautun kaya suna jira a yi musu saboda sai an bi layi a yanzu,” inji shi.

Ya ce a dalilin haka masu masana’antun sarrafa roba na dawo da ma’aikatansu da suka sallama a baya, saboda sun kara tsawon lokacin da ake yin aiki, inda a cewarsa a yanzu suke aikin karba-karba a tsawon awa 24.

Ya ce sun farfado da wasu injunansu da a baya suka dakatar da amfani da su, yayin da wadansu daga cikinsu ke kafa sababbin injuna don su ci gajiyar haka. “Kiranmu ga gwamnati a yanzu shi ne ta sa baki kan karin kudin wutar latanki da ake yi mana kamar yadda gwamnatocin waje ke yi wa masu masana’antunsu,” inji shi.

Ya ce idan gwamnati ta dauki matakin yi musu rangwame, hakan zai ba su damar gogayya da takwarorinsu na gida ’yan asalin China da kuma Indiya.

Wani jagora a harkar, Alhaji Lawal Madaki ya ce dabi’a ce kawai ta rashin kishin kayan gida da ’yan Najeriya ke da ita ta fifita kayan waje a kan na kasarsu ba wai lallai don na wajen ya fi na Najeriya inganci ba ne. Ya bukaci gwamnati ta taimaka wa musu harkar sarrafa sharar roba wadanda ya ce sun rufa wa matasa masu yawa asiri ta hanyar karfafa ayyukan yi da kuma bunkasa tattatalin arzikin kasa maimakon karbar haraji kadai, kamar yadda ya yi bayani