Rufe kan iyakoki alheri ne ga ci gaban tattalin arziki – Adahama

Alhaji Sa’idu Dattijo Adahama Fitatcen dan kasuwa ne, masani kan harkar masana’antu da tattalin arziki. A tattaunawarsa da Aminiya  ya ce rufe kan iyakoki da Gwamnatin Tarayya ta yi alheri ne ga tattalin arziki tare da inganta tsaro:   Ga ka a Cibiyar Binciken   Aikin Gona (IAR) ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya me […]

Rufe kan iyakoki alheri ne ga ci gaban tattalin arziki – Adahama

Alhaji Sai’du Dattijo Adahama

Alhaji Sa’idu Dattijo Adahama Fitatcen dan kasuwa ne, masani kan harkar masana’antu da tattalin arziki. A tattaunawarsa da Aminiya  ya ce rufe kan iyakoki da Gwamnatin Tarayya ta yi alheri ne ga tattalin arziki tare da inganta tsaro:

 

Ga ka a Cibiyar Binciken   Aikin Gona (IAR) ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya me ya kawo ka?

Na zo ne domin gayyata da cibiyar ta yi min, na in gabatar da kasida a kan farfado da noman auduga a Najeriya.

Wani abu da ka yi magana a kai shi ne rufe kan iyakokin kasar nan da Gwamnatin Tarayya ta yi mene ne amfanin da manoma za su samu dangane da haka?

Ai rufe kan iyaka ba wai ya tsaya a kan manoma ba ne kawai alheran da kulle kan iyakokin kasar nan ya kawo ba su da iyaka. Mu fara da ingantuwar tattalin arziki da kasar nan ta samu, ko ba komai a yanzu da aka rufe kan iyakokin, kai shaida ne cewa an samu raguwar tashin-tashina saboda an toshe hanyar da suke shigo da duk wani makami, ai ka ga wannan ma nasara ce.

Don haka ita Gwamnatin Tarayya shirye-shirye da take yi shi ne ta gyara dukkan kafofin shiga na kasar nan ya zamana duk inda ake shigowa da kaya an tantance shi kafin a shigo da shi.

Haka shinkafar da ake shigowa da ita daga kasashen waje wadda ta dade a ajiye ta dauki tsawon shekaru bayan an yi mata  feshi iri-iri, mai haifar da cututtuka da suke addabar al’umma a yanzu an samu raguwar haka, inji masana kiwon lafiya, saboda komawa ga amfani da shinkafar gida wadda ba ta da sinadarai ko magunguna don haka wannan alheri ne.

Kuma rufe kan iyakaokin kasar nan zai dawo wa matan karkara masu samar da man girki aiki yi wanda a da matan karkara su ne masu samar da man girki kamar man gyada da man kade da sauransu. Amma shigowa da man girki da kasar Brazil da ake yi ya kashe musu tasu sana’ar.

Haka kuma durkushewar kamfanoninmu barin kan iyakokimu a bude ya kara haifar da samar da rashin aikin yi, ya yawaita a kasa. Gwamnati ba ta rufe kan iyakokin kasar nan ba ne, cewa ta yi a daina shigowa da kaya ta hanyar da ba ta dace ba.

To a karshe mene ne ra’ayinka kan haka?

Ra’ayina ina goyon bayan rufe kan iyakokin kasar nan dari bisa dari har sai gwamnati ta gama shirinta na tantance duk wani abu da za a shigo mana da shi kafin a shigo da shi.

Kuma kulle kan iyaka  zai kara  inganta samar da haraji ga gwamnati lokacin shigo da duk wani kayan kasar waje. Don haka ya kamata mu hada kai dukkan mu ’yan Najeriya mu ba Gwamnatin Tarayya cikekken  goyon baya a kan rufe iyakokin kasar nan da ta yi don samun karuwar tattalin arziki. ’Yan kasa su samu aiki yi, mu  inganta rayuwarmu mu  daina dogaro da kasashen waje, mu dogara da kanmu. Matasanmu su samu aikin yi a kasa, domin rashin aikin yi shi ne yake kara haifar da tashe-tashen hankali da ake fama da shi.