Rufe kasuwar Abuja Market ya durkusar da kasuwanci a Jos – Nalele

Mataimakin Shugaban ’Yan Kasuwar karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato Alhaji Habibu Lawal Nalele ya ce rufe Kasuwar Abuja Market da gwamnatin jihar ta yi bayan tashin tagwayen bama-bamai a kusa da kasuwar a kwanakin baya, ya durkusar daharkokin kasuwanci a garin Jos. Alhaji Habibu Nalele ya bayyana haka ne a lokacin da […]

Rufe kasuwar Abuja Market ya durkusar da kasuwanci a Jos – Nalele
Rufe kasuwar Abuja Market ya durkusar da kasuwanci a Jos – Nalele

Mataimakin Shugaban ’Yan Kasuwar karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato Alhaji Habibu Lawal Nalele ya ce rufe Kasuwar Abuja Market da gwamnatin jihar ta yi bayan tashin tagwayen bama-bamai a kusa da kasuwar a kwanakin baya, ya durkusar da
harkokin kasuwanci a garin Jos.
Alhaji Habibu Nalele ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, inda ya ce ya kamata gwamnatin Jihar Filato ta tausaya wa jama’ar da ke kasuwanci a kasuwar ta sake bude ta.
Ya ce idan aka ce ba za a bude kasuwar ba, to za a dada jefa jama’ar Jos da dama a cikin wani mawuyacin hali. Kuma abin zai ci gaba da shafar harkokin bankunan da ke kan titin Ahmadu Bello Way. “Don ya kamata gwamnatin Filato ta tausaya wa ’yan kasuwar ta
sake bude ta,” inji shi.
Habibu Nalele ya ce tun daga lokacin da aka kone babbar kasuwar Jos inda ’yan kasuwar suka yi asarar biliyoyin Naira suka shiga cikin mawuyacin hali, kuma har zuwa wannan lokaci ’yan kasuwar ba su gama farfadowa daga gobarar babbar kasuwar ba.
Ya ce ’yan kasuwa masu son zaman lafiya ne, domin idan wata fitina ta tashi su ne ake fara cutarwa. Don haka ya yi kira ga ’yan kasuwar Jos su kara hakuri su ci gaba da zaman lafiyar da aka sansu da ita.