Rufe kasuwar mil 12 a Legas ya haifar da faduwar farashin kayan miya a Ibadan

Umarnin rufe kasuwar Mil 12 da Gwamnatin Jihar Legas ta bayar a dalilin kazamin fadan kabilanci da aka yi a ranar Juma’ar da ta gabata ya sa manyan motoci dauke da kwandunan tumatir da tattasai da albasa sun juya akala zuwa wasu kasuwanni a jihohin da ke makwabtaka da Legas, domin hanzarta sayar da irin […]

Rufe kasuwar mil 12 a Legas ya haifar da faduwar farashin kayan miya a Ibadan
Rufe kasuwar mil 12 a Legas ya haifar da faduwar farashin kayan miya a Ibadan

Umarnin rufe kasuwar Mil 12 da Gwamnatin Jihar Legas ta bayar a dalilin kazamin fadan kabilanci da aka yi a ranar Juma’ar da ta gabata ya sa manyan motoci dauke da kwandunan tumatir da tattasai da albasa sun juya akala zuwa wasu kasuwanni a jihohin da ke makwabtaka da Legas, domin hanzarta sayar da irin wannan kaya ga mabukata kafin su lalace. Hakan ne ya janyo cunkoson irin wannan kaya da faduwar darajarsu a kasuwar Sasa da ke Ibadan.
Wakilinmu ya ziyaraci kasuwar ta Sasa a ranar Talatar da ta gabata, a inda ya gane wa idanunsa jerin layin manya da kananan motoci dauke da buhuna da kwandunan kayan tumatir da tattasai da suke jiran a sauke kayan kafin su kai ga lalacewa. Tanko Maisamari, yana daga cikin fataken irin wannan kaya da ya juyo akala daga Legas zuwa Ibadan, ya ce: “Akwai manyan motoci masu yawa da suka yo lodin kayan tattasai da tumatir daga Arewacin kasa zuwa Legas amma suka kasa shiga cikin kasuwar Mil 12 domin saukewa a dalilin rufe kasuwar da aka yi, wanda dole ce ta sa muka karkato da akala zuwa nan Ibadan domin guje wa rubewar irin wannan kaya. Haka kuma akwai da yawa daga cikin irin wannan kaya da suka lalace gaba daya.”
Mataimakin sakatare na kungiyar masu kayan miya a kasuwar Sasa, Alhaji Iliyasu Bala Muhammed, cewa ya yi: “Alal hakika akwai da yawa daga cikin fataken kayan miya da suka yo lodin kayansu daga Arewa zuwa Legas amma suka juyo da kayansu zuwa nan kasuwar Sasa da ke Ibadan saboda umarnin rufe kasuwar Mil 12 da gwamnati ta yi. Wannan ne ya janyo cunkoso da faduwar darajar kayan a cikin kasuwarmu saboda sun iso gare mu ne a daidai lokacin da irin namu kayan ba su kare ba. Hakan ya janyo hasarar kudi masu yawa da wasu fatake suka yi.”
Da yake amsa wata tambaya Alhaji Iliyasu Bala, ya ce: “Lallai ne farashin irin wannan kaya zai tashi sama ne a dalilin karancinsu a can Legas kawai amma abun ba haka yake a nan Ibadan ba, domin tun farko akwai wadatattun kayan a tare da mu da muka samu kari na ba zata; wanda ya janyo faduwar farashinsu a nan Ibadan. Duk da haka mun sa hannu biyu mun karbe su domin dukkansu ’yan uwanmu ne kuma abokanan sana’armu ne da suka fito daga Arewacin kasa, wanda bai kamata mu zuba ido muna ganin suna yin hasarar dukiyarsu ba tare da mun kawo dauki ba.”
kungiyar ’yan kasuwar ta Sasa, sun jajanta wa fataken kayan miya, musamman wadanda aka kulle kayansu a cikin kasuwar Mil 12, wanda zai yi sanadin rubewa da lalacewar kayan baki daya. “Muna rokon Allah Ya mayar masu da alheri kuma muna yin kira ga Gwamnatin Jihar Legas da ta duba wannan al’amari da idon rahama, ta bude kasuwar Mil 12 domin lura da irin illar da rufe kasuwar zai haifar ga dimbin mutane.