Rufe majalisa na nuna hadarin da kasar nan ke ciki – Masari

Tsohon Shugaban Majalisar Wakilai kuma mai neman takarar gwamnan Jihar Katsina a karkashin jam’iyyar APC Alhaji Aminu Bello Masari, ya zanta da wakilinmu game da yadda yake kallon daukar matakin rufe majalisa da jami’an tsaro suka yi a watan jiya da kuma sauran batuwa. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Yaya kake kallon abin da […]

Rufe majalisa na nuna hadarin da kasar nan ke ciki – Masari
Rufe majalisa na nuna hadarin da kasar nan ke ciki – Masari

Tsohon Shugaban Majalisar Wakilai kuma mai neman takarar gwamnan Jihar Katsina a karkashin jam’iyyar APC Alhaji Aminu Bello Masari, ya zanta da wakilinmu game da yadda yake kallon daukar matakin rufe majalisa da jami’an tsaro suka yi a watan jiya da kuma sauran batuwa. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Yaya kake kallon abin da ya faru da ya kai har jami’an tsaro suka hana kakakin majalisar wakilai da sauran ‘yan majalisa shiga ginin majalisar?
Masari: Akwai alamar tambaya a cikin al’amarin. Wannan abin da ya faru a majalisar tarayya ya nuna irin shugabancin da ake yi a kasar nan. Wannan ya gwada irin hadarin da ke ciki a kyale irin wannan shugabanci ya kara kwana daya daga ranar 29 ga watan Mayu. Abin da wannan shugabanci ke yi kare ba zai ci ba. Wannan yayi kama da abin da ya faru lokacin da kwamishinan ‘yandansan Jihar Ribas ya hana gwamnan jihar shiga gidan gwamnati. Har ila yau duk dai a jihar aka ce mutun biyar sun kori sama da mutane 20 a majalisa. Kuma duk wannan gwamnati ce take amfani da ‘yansanda da sauran ma’aikatan tsaro ayi wannan.
Aminiya: Baka ganin an dauki wancan matakin ne saboda kare lafiyar shugaban majalisa da sauran ’yan majalisa?
Masari: Tun lokacin da aka janye wa kakakin majalisar jami’an tsaron da ke tsare lafiyarsa, yakamata shi shugaban majalisar dattawa ya rufe majalisar.A ce an hana shugaban majalisar dokoki shiga majalisa Edecutibe Coup (Juyin mulki ne).
Aminiya: Wasu na cewa jami’an tsaron suna bakin aikinsu ne, saboda haka ba laifinsu ba ne?
Masari: Shi azzalumi idan ya gama zalumtar wanda baka so, to kanka zai dawo. Idan ba kawar da wannan gwamnatin aka yi ba, lallai sai ta rusa Najeriya. Lokacin da nake kakakin majalisa, gwamnatin Amurka ta hannun masu leken asiri da sanin al’amuran yau da kullum ta rubuto mana,ta ce ga abubuwa nan daga daya zuwa biyar kuna yi, idan ba ku daina kaza da kaza ba, ku aiwata da kaza da kaza kafin shekarar 2015, Najeriya tana iya rushewa. Duka abubuwan da suka ce za su abku ba su abkun ba? Cikin su har da wannan Boko Haram din.
Aminiya: Ba ka ganin sojojin kasar nan suna iya kokarinsu wajen shawo kan matsalar?
Masari: Ana kashe makudan kudi akan horar da sojan Najeriya, bayan samun lambobin yabo daga kasashen duniya akan iya yaki, amma abin mamaki a ce wai sai masu amfani da bindigar toka ne za’ace sun kwato wuri daga hannun wadanda suka mamaye su kasan akwai magana ce. Amma a ce Dantauri yayi aikin da soja ne zaiyi.
Aminiya: Wane kira za ka yi ga al’umma?
Masari: Magoya bayanmu su zamo masu bin doka da oda, kada su biye wa masu neman tashin hankali da su. Kuma furucin da gwamnan Jihar Katsina Barrister Shema ya yi akan batun kyankyasan siyasa, bai kamaci shugaba irinsa yana irin wannan furucin ba. Misali abin da ya faru a tsakanin magoya bayanmu da na jam’iyyar PDP a garin Karofi, inda aka cika jaka da yashi aka rufe masu hanya a lokacin da suka zo wucewa a garin. Wannan ne ya jaza abinda ya faru, amma jam’iyya PDP ta ce magoyabayanmu sun kashe mata mamba. Batun ba haka yake ba.
Aminiya: Wadanne abubuwa za ka ba fifiko idan aka zabe ka gwamnan Jihar Katsina?
Masari: Zan bai wa ilimi da aikin gona muhimmanci. Wadannan su ne manyan abubuwan da zan fara ba fifiko har in aka zabe ni, sannan sauran abubuwa su biyo baya.