Rufe Twitter: Yadda ’Yan Najeriya Suka Yi Asara, Gwamnati Ta Ci Riba
Gwamnati za ta samu makudan kudade daga harajin da kamfanin Twitter zai rika biyanta nan gaba.
Domin sauke shirin latsa nan
A kwana akalla 220 da gwamnatin Najeriya ta rufe harkokin kafar sada zumunta ta Twitter, ’yan kasar sun tafka asarar makudan kudade, a yayin da gwamantin kuma ta ci gagarumar riba a sakamakon matakin da ta dauka.
Masana sun yi bayanin irin makudan kudaden da Gwamnatin Tarayya za ta rika samu daga harajin da za ta rika karba daga hannun kamfanin Twitter a sakamakon amfanin da ’yan Najeriya suke yi da kafarsa, domin gudanar da harokinsu na kasuwanci da kuma sadar da zumunta.