Ruftawar gadar jirgin kasa ta yi ajalin mutum 23 a Mexico

Akalla mutum ne 23 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 70 suka jikkata daren Litinin sakamakon ruftawar wata gadar jirgin kasa mai hanyar sama a Kudancin birnin Mexico. Magajin garin birnin Mexico, Claudia Sheinbaum, ya ce hatsarin ya auku ne yayin da wani ginin kankare ya rufta a kan gadar yayin da jirgin kasan […]

Ruftawar gadar jirgin kasa ta yi ajalin mutum 23 a Mexico

Yadda gadar ta rufta da jirgin kasa a Mexico

Akalla mutum ne 23 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 70 suka jikkata daren Litinin sakamakon ruftawar wata gadar jirgin kasa mai hanyar sama a Kudancin birnin Mexico.

Magajin garin birnin Mexico, Claudia Sheinbaum, ya ce hatsarin ya auku ne yayin da wani ginin kankare ya rufta a kan gadar yayin da jirgin kasan ke tafiya a kanta.

Claudia ya ce, “abin bakin ciki mutum 23 ne suka rasa rayukansu, ciki har da yara.

“A halin yanzu, ana ci gaba da aikin ceto kuma za a gudanar da bincike domin gano musabbabin aukuwar hadarin,” a cewarsa.

Mahukunta a ranar Talata sun sanar da cewa nan take aka garzaya da mutum 49 daga cikin wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

Hoton bidiyon da wani gidan talabijin na yankin ya hasko ya nuna yadda tarragon jirgin ke reto a jikin gadar sarkake cikin wasu wayoyi na karfe, inda goshin jirgin ke kallon kasa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, a shekarar 2012 ce aka fara amfani da gadar jirgin kasa ta Metro 12.

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa

Masu zanga-zanga sun tare babbar hanyar Abuja kan matsalar tsaro

Janar Rabe Abubakar ya rasu a hannun ’yan bindiga