Ruftawar gini ta kashe uwa da ’ya’yanta 5 a Katsina
Wannan tsautsayi ya rutsa da mutum goma, amma abin baƙin ciki, shida daga cikinsu sun rasu.
Wata uwa da ’ya’yanta biyar sun riga mu gidan gaskiya a dalilin ruwan sama kamar da bakin ƙwarya wanda ya janyo ruftawar ginin gidansu a ƙauyen Dankama da ke Karamar Hukumar Kaita a Jihar Katsina.
Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe biyu na dare a ranar Litinin yayin da waɗanda ajalin ya katsewa hanzari ke tsaka da barci.
- Kotu ta hana jagoran adawa Maurice Kamto takarar shugaban ƙasa a Kamaru
- Mulkin Tinubu ya fi na Buhari muni — Maina Waziri
Bayanai sun ce wasu mutum huɗu waɗanda su ma lamarin ya rutsa da su an gaggauta miƙa su asibiti domin samun kulawa.
Magidancin da aka yi wa wannan babban rashi, Muhammad Sani Garba, yayin ganawa da manema labarai ya ce ba ya gida lokacin da tsautsayin ya auku.
“Wannan tsautsayi ya rutsa da mutum goma, amma abin baƙin ciki, shida daga cikinsu sun rasu. A halin yanzu, mutum huɗu suna asibiti ana duba lafiyarsu,” in ji shi.
“Na ɗauki wannan a matsayin ƙaddara daga Ubangiji. Allah Ya jiƙansu, Ya sanya su a Aljannar Firdausi,” a cewarsa.
Daraktar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Katsina (SEMA), Hajiya Binta Dangani, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa ma’aikatan hukumar sun ziyarci wurin da lamarin ya faru domin tantance halin da ake ciki da ɗaukar matakin gaggawa.