Ruftawar gini ta kashe yara 6 a Jigawa

Daga cikin wadanda suka mutu, guda 4 duk na mutum ɗaya ne.

Ruftawar gini ta kashe yara 6 a Jigawa

Ruftawar gini ta kashe yara 6 a dalilin ruwan sama da aka tafka kamar da bakin kwarya a Karamar Hukumar Kirikasamma da ke Jihar Jigawa.

Jami’in yaɗa labarai na ƙananan hukumomin Malam Madori da Kirikasamma, Alhaji Musa Muhammad ne ya bayyana hakan a zantawarsa da wakilinmu ta wayar tarho.

Ya bayyana cewa wani mazaunin ƙauyen Gamji, Malam Yahaya Gamji, ya ce ‘ya’yansa 4 sun mutu bayan da gidansu ya rufta da tsakar dare a ƙauyen Gamji da ke unguwar Turabu ta Karamar Hukumar Kirikasamma.

Ya ce, daga cikin yaran da suka mutu, guda 4 duk na mutum ɗaya ne mai suna Na Kayuwa Gamji.

Kazalika, an samu rahoton mutuwar sauran mutum biyun ne sakamakon ruwan sama ba ƙaƙƙautawa da ya sauka, lamarin da ya janyo ruftawar gidajen jama’a a ƙauyen Fandin da ke Karamar Hukumar Kirikasamma.

Wani mai mai riƙe da sarautar gargajiya, Malam Umar Yakubu Mukaddas,  ya bayyana cewa mutanen biyu 2 da suka rasu a Fandin ginin ɗakin ne ya rufta a kansu.

Ya ƙara da cewa, “ambaliyar ruwa ta mamaye gonakinmu na shinkafa saboda ruwan saman da ya sauka mai yawa ne.”