Ruftawar gini ta laƙume rayukan mutum 10 a Ibadan

An ciro mutane 10 daga cikin baraguzan benen da ya ruguje, yayin da aka ceto mutane bakwai da ransu.

Ruftawar gini ta laƙume rayukan mutum 10 a Ibadan

Mutane 10 ne ake fargabar sun mutu sakamakon ruftawar wani bene a safiyar ranar Alhamis a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Babban Manajan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Oyo, Mista Yemi Akinyinka ne ya tabbatar da hakan yayin ganawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN).

Akinyinka ya ƙara da cewa wasu mutum bakwai sun samu raunuka a ruftawar ginin wanda rahotanni suka ce ya faru da misalin ƙarfe 2:00 na tsakar dare a unguwar Jegede Olunloyo da ke Ibadan a ranar Alhamis.

Ya ce, Hukumar ta samu kira mai cike da damuwa game da ruftawar ginin da misalin ƙarfe 2:00 na tsakar daren inda nan take ta tura jami’ai zuwa wurin.

“Hukumar kashe gobara ta jihar Oyo ta samu kiran waya da misalin ƙarfe 2 na dare, a unguwar Jegede Olunloyo, a Ibadan inda aka ciro mutane 10 daga cikin baraguzan benen da ya ruguje, yayin da aka ceto mutane bakwai da ransu,” in ji shi.

A cewar babban manajan, ana ci gaba da aikin ceto waɗanda ake zargin sun maƙale a ƙarƙashin baraguzan ginin.