Ruftawar ginin coci ta kashe fasto a Binuwai

Ginin cocin Sunansa ya rufta inda ya kashe daya daga cikin fastocin cocin a Jihar Binuwai

Ruftawar ginin coci ta kashe fasto a Binuwai

Ginin cocin Dunamis ya rufta inda ya kashe wani fasto tare da jikkata masu ibada garin Makurdi, hedikwatar Jihar Binuwai.

Shaidu sun shaida wa wakiliyarmu cewa bayan kammala ibadar a ranar Litinin da dare faston da wasu mutane suka ci gaba da tasu ibadar kafin rushewar ginin da asubahi.

Wani shaida mai suna Kole, ya ce, “daga baya an tafka ruwan sama, don haka ba su iya tafiya gida ba, suka ci gaba da ibada, har zuwa misalin karfe uku na asuba da ginin cocin ya rufta a kansu, ya yi ajalin faston.”

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Binuwai, Batholomew Onyeka, ya tabbatar da rasuwar tare da cewa wasu mutum hudu sun samu raunuka a sakamakon rushewar ginin cocin da ke yankin North Bank.

Wani dan unguwar ya ce an garzaya asibiti da wasu mutum hudu da ke ibada tare da faston a lokacin da ginin ya rufta a kansu, suka samu raunuka.

Kawo yanzu dai ba a bayyana sunan faston ba, amma wasu makwabtan cocin sun ce dan asalin Jihar Kogi ne.

DAGA LARABA: Yadda Almajiri Ya Zama Mabaraci

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe

Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato