Ruftawar ginin daki ya kashe matar aure a Jigawa

Wata matar aure mai kimanin shekaru 20 ta rasa ranta sakamakon ruwan sama da aka yi tayi wanda ya yi sanadiyyar rushewar dakinta, da ke Karamar Hukumar Kafin Hausa a jihar Jigawa. Marigayiyar mai suna Fatsima Musa tana tare ne da mijinta, Musa Awaisu, mai shekaru 27, a cikin dakin su lokacin da al’amarin ya faru. […]

Ruftawar ginin daki ya kashe matar aure a Jigawa

Wata matar aure mai kimanin shekaru 20 ta rasa ranta sakamakon ruwan sama da aka yi tayi wanda ya yi sanadiyyar rushewar dakinta, da ke Karamar Hukumar Kafin Hausa a jihar Jigawa.

Marigayiyar mai suna Fatsima Musa tana tare ne da mijinta, Musa Awaisu, mai shekaru 27, a cikin dakin su lokacin da al’amarin ya faru.

Ma’auratan, wanda ke zaune a kauyen Aune an garzaya dasu asibiti a lokacin da lamarin ya afku, inda nan take likitoci suka tabbar da mutuwar matar.

Wani wanda abin ya faru akan idonsa, ya ce lamarin ya farune a cikin dare yayin da ake mamakon ruwan sama, inda aka garzaya dasu asibiti cikin mawuyacin hali.

Mai Magana da yawun bakin rundunar ’Yan sanda na jihar, SP Abdul Jinjiri ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda ya ce tuni aka mika gawar zuwa ga iyalanta don yin sutura.