Ruftawar rami ta kashe masu haƙar ma’adanai 22 a Adamawa da Taraba

Dukkan masu haƙar ma’adinai 22 da suka maƙale a cikin ramin ana kyautata zaton sun mutu, wani yanki da ake kira Buffa zone a Gashaka

Ruftawar rami ta kashe masu haƙar ma’adanai 22 a Adamawa da Taraba

Aƙalla masu haƙar ma’adanai 22 ne ake kyautata zaton sun mutu sakamakon ruftawar wani rami da ake haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, da ke cikin wani gandun daji na ƙasa wanda ya ƙunshi ƙaramar hukumar Gashaka a jihar Taraba da kuma Ƙaramar Hukumar Toungo a Jihar Adamawa.

Adamu Jamtare, wani mai haƙar ma’adinai daga Gashaka ya bayyana cewa da yawa daga cikin waɗanda suka rasu sun fito ne daga garin Jamtare da ke Ƙaramar hukumar Gashaka a Jihar Taraba.

“Suna haƙar zinare a wani yanki da ake kira Buffa zone a cikin gandun dajin Gashaka-Gumti, wanda ya mamaye sassan Gashaka da Toungo. Dukkan masu haƙar ma’adinai 22 da suka maƙale a cikin ramin ana kyautata zaton sun mutu,” in ji shi.

Shugaban Ƙaramar hukumar Toungo, Injiniya Suleiman Toungo, ya tabbatar da cewa an gano gawarwakin ma’aikatan haƙar ma’adanai biyar, duk da cewa bai da tabbas kan adadin da aka binne har yanzu.

Ya ce, al’amarin da ya shafi masu haƙar ma’adinai daga sassa daban-daban na Nijeriya da suka haɗa da Zamfara da Adamawa ya faru kusan wata guda da ya gabata.

Duk da yankin akwai jami’an tsaro masu sintiri a dazukan, an ci gaba da gudanar da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a yankunan, wanda galibi ana gudanar da su cikin dare ne. “Ya zuwa yanzu an gano gawarwaki biyar,” in ji shi.

Gandun namun daji na ƙasa, wanda aka sani da albarkatun ma’adinai, ana asarar rayuka da dama a cikin ‘yan shekarun nan saboda ayyukan haƙar ma’adinai marasa tsari.

Wani mazaunin ƙauyen Tila, da yake bayani wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa kimanin masu haƙar ma’adinai 70 ne suka rasa rayukansu a irin wannan lamari a bara, duk da cewa har yanzu ba a kai ga rahoton waɗanda lamarin ya rutsa da su ba.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya tabbatar da rahotanni biyu na baya-bayan nan kan asarar rayuka sakamakon ruftawar ramin.

 

Sanata Barau ya kai ziyarar ta’aziyya a Kano

Mun kusa kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya — Tinubu

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Gombe, ya rasu

Matatar Dangote ta rage farashin man fetur