Ruguza jiragen da ake satar mai ne mafita – Admiral Ombu

Bayis Admiral Godwill Ombu babban hafsa ne na sojan ruwa, wanda bayan ya yi murabus yake zaman kansa, ya shaida wa Aminiya sai an yi da gaske don a magance satar mai a kasar nan, musamman ya bukaci a rika konewa ko ruguza jiragen da ake satar man da su idan ana so a shawo […]

Ruguza jiragen da ake satar mai ne mafita – Admiral Ombu
Ruguza jiragen da ake satar mai ne mafita – Admiral Ombu

Bayis Admiral Godwill Ombu babban hafsa ne na sojan ruwa, wanda bayan ya yi murabus yake zaman kansa, ya shaida wa Aminiya sai an yi da gaske don a magance satar mai a kasar nan, musamman ya bukaci a rika konewa ko ruguza jiragen da ake satar man da su idan ana so a shawo kan matsalar:

Aminiya: Mene ne aikin sojan ruwan Najeriya?

Admiral Ombu: Aikin sojan ruwan Najeriya uku ne: Sanin iyakar ruwan kasa, yaki don kare martabar kasa da kuma diplomasiyya wato tattaunwa. Bayani a nan shi ne kare gabar ruwa da ya kai mil 24 a cikin ruwan teku da bin dokar Najeriya sau da kafa. Sannan sojan kasa da na sama da na ruwa ne kadai alhakin kare kasa baki daya yake wuyansu. Amma daukar wani kamfani ya kare gabar ruwan kasar nan, (kamar yadda aka yi a zamanin gwamnatin Jonathan da ta gabata) lallai yi wa dokar aikin sojan ruwa katsalanda ne. Kuma haka abin yake a kowace kasa ta duniya. A takaice Najeriya ba ta bukatar masu gadin gabar ruwanta. Amma lallai ne a tabbatar da yawan sojan sun isa aikin da ke gabansu. kasar da ta ci gaba ne ke nada masu gadin gabar ruwa wato (Coast Guard). Domin mu kasa ce mai tasowa, ba mu karade yankin Afirka ta Yamma ba, balle mu dauki ’yan kasuwa sojan haya (su yi mana gadin iyakar ruwanmu). Sojan ruwan Najeriya na kwashe yawancin lokacinsu ne a gida a kan kasa ba a cikin teku ba, wanda hakan bai dace ba. Babban aikin sojan ruwa lokacin da ake zaman lafiya ba yaki, shi ne tsaron gabar ruwa. Ban yarda da cewa ya dace a kafa kamfanin ’yan kasuwa su rika gadin gabar ruwa ba, domin muna da rundunar sojan ruwa da ta shekara 50 tana aiki. Duk kasar da take aiki da kamfanin gadi a gabar ruwanta da ba su da jiragen ruwa da jiragen sama helkwafta, ita ce kuma take da sojan ruwa. In dai ana da kudin za a ba kamfanin, me zai hana a inganta sojan ruwa. Najeriya ba ta bukatar kamfanin gadin bakin gabar ruwanta.
Aminiya: Ko wannan na ci wa sojan ruwan Najeriya dudduge?
Admiral Ombu: Ni dai matsayina shi ne a inganta sojan ruwan Najeriya. Kuma lallai wannan yin karan -tsaye ne da cin dudduge da ma komai za a kira shi.
Aminiya: Yaya za a yi a cimma nasara?
Admiral Ombu: Yawancin jiragen yakin Najeriya an kera su ne fiye da shekara 30. Ganin yadda aka ci gaba a harkar fasaha, jiragen na tsaye ne cik, ba su iya shiga teku. An dai gaya min cewa sun fara kera sababbin jirage. Ya dace ne sojan ruwa ya kwashe makonni ko watanni yana atisayen yaki a cikin teku amma ba a kan tudu ba. Hakan zai rage almundahanar da ake ta tafkawa a kan ruwan kasar nan. A duk duniya soja kadai ke daukar manyan makamai da za su iya wuni suna harbi don kare kasa, ba farar hula dan kwangila dauke da kananan bindigogin da ake rataya a kafada ba.
Aminiya: Yaya kake ganin za a bi a magance satar mai da manyan jiragen ’yan bumburutu ke yi?
Admiral Ombu: A samar da manyan makamai a harbi jirgi daya ya yi daram ya fashe, Turawa da ’yan kasa barayin mai su sheka barzahu, shi kuma jirgin ya kwana ya wuni ya na ci da wuta, duniya ta ji kuma ta gani, sai satar mai ta tsaya cik.
Aminiya: Mene ne aikin masu tsare gabar ruwa na ’yan kasuwa Coats Guard?
Admiral Ombu: Coast Guard dabam, suna tallafa wa sojan ruwa a aiki ne don aiki ya yi musu yawa. Aikinsu shi ne kula da kananan jirage da ceton mutane a ruwa. Kamfanin ’yan kasuwa mai gadin gabar ruwa daban. Saboda gazawar sojan ruwa na yin sintiri, shi ya sa kamfanonin mai suka fara hayar ’yan kasuwa su yi gadin dukiyoyinsu. In ni ne Babban Hafsan Sojan Ruwa, zan tsayar da daukar sojojin haya don a inganta sojan ruwa. A 1980, lokacin da babu barayin mai sosai, ba mu da sojan haya. Matsalar tsaronmu ba ta kai ta tabarbarewar kasar Somaliya ba.
Aminiya: Mene ne ra’ayinka kan kwangilar da aka ba tsohon shugaban ’yan ta’addan Neja-Delta mai suna Gobernment Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo?
Admiral Ombu: Ban san cikakkaen lamarin ba balle in ba da amsa a kai.
Aminiya: Ta yaya sojan ruwa ke samun sababbin makamai?
Admiral Ombu: Ba sojan ruwan da ke sayo makamai da kansu ba. Yadda ake yi sh ine, sojan ruwa za su rubuta wa Ma’aikatar Tsaro ga irin jirage da makamai da kayan aikin da suke bukata. Sannan ma’aikatar ta sa a cikin kasafin kudinta na shekara. In an yi kasafi an amince a sayo, sai a tura soja su je su tuko jiragen da makaman da aka sayo.
Aminiya: Mene ne aikin Hukumar NIMASA?
Admiral Ombu: Amma ya dace a san cewa ita hukumar gwamnati da ake ce wa NIMASA tana da alhakin kula da ba da lasisin jiragen farar hula masu kamun kifi da sauran jiragen fito kanana da na shakatawa ne. Kowa na iya hulda da su. Ana iya ba jirgin shawagi na NIMASA sojan ruwa da bindiga don maganin barayin teku. Jiragen NIMASA kanana ne, ba za su iya yin mako a cikin teku ba. Sannan manyan makamai ake aiki da su a cikin teku, ba kanana irin su AK 47 ba. Amma ba a yarda su NIMASA su dauki makami ba. Misali kamar yadda ake ba bankuna ’yan sanda su yi musu rakiya.
Aminiya: Ko kwangilar da NIMASA ta ba Tompolo ya dace?
Admiral Ombu: Ban sani ba, amma na san kamfanin GLOBAL WEST ya samu kwangila daga NIMASA don samar da jiragen ruwa. Kwangilar ita ce ta samar da jiragen ruwa da yi musu garambawul. Lallai laifi ne wani ya gudanar da kamfanin in ba ma’aikacin NIMASA ba ne. A tuna cewa kafin a kafa NIMASA, akwai hukumar kula da jiragen ’yan kasuwa wato Nigerian Maritime Authority, (NMA) don kula da lafiyar jiragen da bin dokar fito a ruwa. Kwatsam sai aka kafa NIMASA inda aka rikita harkar tsaro don an ba su ikon yin aikin da asali alhakin sojan ruwa ne. Wannan ne ya kambama yawan aikin ta’addanci, wanda yanzu ya gallabi kowa.
Aminiya: Ko kamfanonin ’yan kasuwa suna tallafa wa don rage ta’addanci a cikin ruwa?
Admiral Ombu: Ba zan iya sani ba, domin na yi ritaya. Akwai matsala kwarai don ana dukan taiki ne, maimakon a doki jaki.
Aminiya: Ta yaya za a cimma tsaro a Najeriya?
Admiral Ombu: Za a iya inganta tsaro ne in an wayar da kan jama’a muhimmancin gina kasa don a daina ta’addanci kuma a tona masu yi. Sannan a sama wa sojojin kasa kayan aiki na zamani.
Aminiya: Mene ne abin da ya taba ba ka mamaki a aikin sojan ruwa wanda ka kai mukami irin na Manjo Janar a sojan kasa?
Admiral Ombu: A 1981 jiragen ruwan Ingila daga Turai suka haro Najeriya da muka farmake su a sukwane, bayan minti goma sai jirgin na Ingila ya yi mana sigina na gargadin cewa mu rage gudu, suka fadi ruwan da muke ciki, irin jirgin da muke ciki da malejin gudun da muke yi. Bayan wasu mintoci goma sai ga jirgin sama helkwafta yana shawagi a bisanmu a tsakar teku. To a yanzu ai an samu ci gaban da ya fi gaban wancan ninki ba ninki. Dole ne Najeriya ta san duk jirgin da ya nufo kasar nan tun yana cikin teku, kafin ya yi barna ko satar mai da sauransu a gabar kasar nan.