Rukuni na 3 na kayan jinkai sun shiga Zirin Gaza
Karin motocin kayan jin kai sun shiga yankin Falasdinawa na Zirin Gaza daga mashigar Rafah ta kasar Masar a safiyar Litinin.
Karin motocin kayan jinkai sun shiga yankin Falasdinawa na Zirin Gaza daga mashigar Rafah ta kasar Masar a safiyar Litinin.
Rukuni na uku ke nan a motocin da suka shigar wa Falasdinawan kayan agaji tun daga ranar Asabar, inda kafin ranar Litinin manyan motoci 34 dauke da kaya abinci da magunguna suka shiga Zirin Gaza daga Rafah.
- ’Yan bindiga sun kashe mutane 9 sun sace wasu a Katsina
- Bayanan sahihancin takardun Tinubu sun yi karo da juna —Kotun Koli
Sama da motocin 10 ne suka samu izinin shiga Gaza a safiyar ta Litinin a a yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa ana bukatar akalla motoci 100 na kayan agaji a kullum a Zirin Gaza mai yawan al’umma miliyan 2.4.
Tun ranar 7 ga watan Oktoba jiragen Isra’ila ke wa Zirin Gaza luguden wuta a matsayin ramuwar gayya kan harin da kungiyar Hamas ta kai mata, inda kungiyar ta kashe mutum 1,400 ta yi garkuwa da wasu 200.
Kawo yanzu dai Isra’ila ta kashe Falasdinawa sama da 4,000 a Gaza, ta jikkata sama da 14,0000 tare da rusa gidajen mutum sama da miliyan daya, ciki har da wuraren ibada da makarantu da asibitoci.
Harin da Isra’ila ta kai da ya kashe fararen hula kimanin 500 a wani asibiti a Kudancin Gaza ya kara jawo mata tofin Allah-tsine daga kasashen duniya.