Rukunin farko na Alhazan Kebbi 426 sun dawo gida
Jirgin kamfanin Flynas da ya ɗauko alhazan ya baro Saudiyya da misalin ƙarfe 3:10 na asubahin ranar Alhamis agogon Najeriya.
Rukunin farko na alhazan Jihar Kebbi su 426 da suka sauke farali a Hajjin shekarar 2026 sun iso Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi a ranar Alhamis.
Jirgin kamfanin Flynas da ya ɗauko alhazan ya baro ƙasar Saudiyya da misalin ƙarfe 3:10 na asubahin ranar Alhamis agogon Najeriya, inda ya sauke su lafiya a babban birnin jihar.
- An kama wanda ya yi wa mahaifinsa dukan mutuwa a Ondo
- ’Yan yi wa ƙasa hidima da soja sun rasu a hatsarin mota a Adamawa
Jami’ai sun bayyana cewa alhazan sun fito ne daga ƙananan hukumomin Koko/Besse da Aliero da Bunza, tare da wasu jami’an gwamnatin jihar da na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kebbi.
Wasu daga cikin alhazan da suka zanta da manema labarai sun bayyana godiyarsu ga Allah bisa nasarar kammala aikin Hajji lafiya.
“Mun gode wa Allah Maɗaukakin Sarki da Ya ba mu damar sauke farali cikin nasara tare da dawowa gida lafiya,” in ji wani daga cikin alhazan.
Sun kuma yaba wa Gwamna Nasir Idris, bisa irin kulawa da tallafin da gwamnatin jihar ta ba su a lokacin aikin Hajji.
A cewarsu, matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka sun taimaka wajen sauƙaƙa musu gudanar da ibadunsu a ƙasa mai tsarki.
Wata tawagar gwamnatin jihar da Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Kebbi ce ta tarbi alhazan a filin jirgin saman tare da wasu jami’ai.
Tawagar ta yaba da haɗin gwiwar da aka samu tsakanin gwamnatin jihar da kamfanin jirgin sama da kuma hukumomin Saudiyya, wanda ya tabbatar da dawowar alhazan cikin tsari da nasara.
“Mun gode wa Allah da Ya kawo mana alhazanmu lafiya. Haka kuma muna yaba wa gwamnatin jihar bisa dukkan goyon bayan da ta bayar domin jin daɗin alhazan,” in ji ɗaya daga cikin jami’an tarbar.
Jami’an filin jirgin saman sun ce an kammala dukkan matakan binciken lafiya da na shige da fice cikin nasara kafin a sallami alhazan.
Iyalan alhazan da masu yi musu fatan alheri sun cika filin jirgin saman domin tarbar su bayan dawowarsu daga ƙasa mai tsarki.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kebbi ta ce ana sa ran ƙarin jirage za su ci gaba da kwaso sauran alhazan jihar cikin kwanaki masu zuwa.