Rumfar kamfe din Jonathan ta rufta a kan manyan baki

Rumfar kamfe din neman sake tsayawa takarar Shugaba Goodluck Jonathan ta rufta da manyan baki a garin Minna fadar Jihar Neja.Manyan bakin da suka hada da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata Anyim Pius Anyim da Ministan Labarai, Mista Labaran Maku da Gwamnan Jihar Neja Dokta Mu’azu Babangida Aliyu na cikin rumfar ta rufta bayan Shugaban kungiyar […]

Rumfar kamfe din Jonathan ta rufta a kan manyan baki
Rumfar kamfe din Jonathan ta rufta a kan manyan baki

Rumfar kamfe din neman sake tsayawa takarar Shugaba Goodluck Jonathan ta rufta da manyan baki a garin Minna fadar Jihar Neja.
Manyan bakin da suka hada da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata Anyim Pius Anyim da Ministan Labarai, Mista Labaran Maku da Gwamnan Jihar Neja Dokta Mu’azu Babangida Aliyu na cikin rumfar ta rufta bayan Shugaban kungiyar Makafi ta Najeriya reshen jihar Neja Alhaji Isah Umar Aliyu ya kammala jawabinsa.
Ruftawar rumfar ta ba matasan da ke wurin taron damar kutsawa har wurin da wadanda suka samu kansu cikin mawuyacin halin domin kwashe musu kaddarori da suka hada da wayoyi da takalma da gwala-gwalai a daida lokacin da jami’an tsaro suka yi tsammanin sun zo taimako ne.
Wakilinmu ya ga wani matashi yana shaida wa dan uwansa cewa “Wallahi na yi sa’ar waya mai tsada da gwal na wata mata a kusa da rumfar da ta rufta wadda aka yi ta domin zaman mutum 700.
Wasu daga cikin wadanda suka tsaya kusa da rumfar sun shaida wa wakilinmu cewa sun ji rumfar ta yi ta bayar da alamar samun matsala kafin ta fadi. Wannan ne ya sa suka yi maza-maza suka bar wurin. Sun ce barinsu wurin ke da wuya al’amarin ya faru.
Wakilin gidan Rediyon Muryar Amurka,  Mustapha Nasiru Batsari wanda ya kasance a rumfar lokacin da al’amarin ya faru, ya shaida wa wakilinmu cewa, “Na gama hira da tsohon Ministan Labarai Farfesa Jerry Gana ke nan na durkusa na mika wa Ministan Labarai Mista Labaran hannu muna gaisawa kafin in yi hira da shi, dagowar da na yi kawai sai na ji kara, in duba damana sai sai na mutane sun zube kasa. Nan da nan jami’an tsaro suka zo wurinmu, suka yi mana zobe da wasu manyan mutane sai da suka tabbatar sun sauke mu kasa lafiya.”
Da yake jawabi a wurin taron jim kadan bayan faruwar lamarin, Gwamna Mu’azu Babangida Aliyu ya gode wa Allah da Ya tsayar da lamarin ba a samu asarar rai ba, inda ya danganta lamarin da kaddara.
Dokta Mu’azu Babangida Aliyu ya kara da cewa, “Wannan abin da ya faru wata alama ce ta samun nasara na kudurin da muka sa a gaba na tabbatar da samu nasarar Jam’iyyarmu ta PDP. Mun gode da kuka saurare mu kuma Allah Ya kai kowa gidansa lafiya.”  
Daraktan Sadarwa na kungiyar Transformation Ambassadors Of Najeriya (TAN) Dokta Udenta Udenta ya bayyana rashin jin dadinsa game da aukuwar lamarin, sai dai ya nuna gamsuwa ganin yadda duk da haka jama’a sun tsaya sai da aka kammala shirin yadda aka tsara tun farko.
Dokta Udenta Udenta ya jajanta wa wadanda al’amarin ya rutsa da su, kuma ya gode wa jama’ar da suka zo daga jihohin Arewa ta Tsakiya da wadanda suka bayar da gudunmawa aka samu nasarar gudanar da gangamin na Minna.
Binciken da wakilinmu ya gudanar a wasu daga cikin asibitocin da aka kai wadanda suka samu rauni, ya gano an sallami Mataimakin Gwamnan Jihar Kogi Mista Yomi Awoniyi da Babba Darekta Mai Kula da Al’amuran Jama’a Malam Tanko Dada da wasu da dama.
Gwamnan Jihar Neja Dokta Mu’azu Babangida Aliyu da matarsa Hajiya Jummai Babangida, sun ziyarci mutanen da suka samu raunuka da aka kwantar a Asibitin kwararru na IBB da ke Chanchaga da Babban Asibitin Minna.