Rundunar JTF ta kama dimbin makamai a Kano ……Da hannun ’yan kasasahen ketare dumu-dumu

Rundunar  jami’an tsaro ta hadin gwiwa da ke Kano ta samu nasarar da ba ta taba samu ba inda ta gano dinbin makamai a yayin wani samame da ta kai  wani gida da wani dan kasar waje yake zaune a Bampai da ke Nasarawa Kano.Da farko dakarun sun fara mamaye wani titi ne kilomita biyar […]

Rundunar JTF ta kama dimbin makamai a Kano ……Da hannun ’yan kasasahen ketare dumu-dumu
Rundunar JTF ta kama dimbin makamai a Kano ……Da hannun ’yan kasasahen ketare dumu-dumu

Rundunar  jami’an tsaro ta hadin gwiwa da ke Kano ta samu nasarar da ba ta taba samu ba inda ta gano dinbin makamai a yayin wani samame da ta kai  wani gida da wani dan kasar waje yake zaune a Bampai da ke Nasarawa Kano.
Da farko dakarun sun fara mamaye wani titi ne kilomita biyar daga hedkwatar  rundunar ‘yan sandan jihar Kano a ranar Litinin da dare, kafin  su binciki wani gida da wani dan kasar Lebanon yake zaune a ciki da ke kan titin Gaya, inda aka samu dinbim bindigogi da bama-bamai da gurnetin da ake jefawa da hannu da makaman harbo jiragen sama da kuma wadansu harsasai masu yawa da ba a baiyyana adadinsu ba da aka binne a karkashin kasa a cikin babban falon gidan.
 Mazauna yankin da suka ga yadda samamen ya kasance sun ce sojoji da yawa ne suka kai samamen.
Wani  wanda shi ganau ne, ya ce fiye da bindigogi kirar AK 47 300  da gurnati fiye  da 200 bindigogi kirar RPG masu yawa da bama-bamai  da  harsasai masu linzami da ke harbo jirgin sama ne aka kwasa a cikin wata motar soja daga a  gidan.
Amma wata majiya daga jami’an tsaro ta ce bindigogi kirarar  AK 47 guda 8 ne kawai aka aka samu a gidan da kuma harsasai masu dinbin yawa da bama-bamai guda 100 da harsashin harbo jiragen sama da kuma wadansu irin  muggan makamai. ‘’ Akwai su da yawa ta yadda ba zan iya lisafa maka su a cikin kankanin lokaci ba. Hasali ma dai maganar nan da nake yi da kai ba mu gama kidaya makaman da aka gano a gidan ba.’’ Inji majiyar.
Mazauna yankin sun ce sai da sojoji suka yi amfani cebur wajen loda harsashen a cikin mota.
Aminiya ta gano cewa,  kai samamen ya biyo bayan kama wani da aka yi ne a wurin binciken ababen hawa, wanda shi kuma ya nuna wa jami’an JTF  ginin da makaman suke jibge a cikinsa.
Makwabtan wurin sun bayyana sunan dan kasar Lebanon din da ke zaune a guidan, amma sun ce wani dan Najeriya da ke zaune a kasar Amurka ne yake da gidan.
A cewar majiyar jami’an tsaron, an boye makaman ne a cikin wani katon sito  da ke karkashin kasa a karkashin  babban falon gidan, inda aka yi wurin shiga ta cikin  wajen ajiye suturu.
Makwabtan sun ce wanda yake zaune a gidan wani dattijo ne  da yake aiki a wani kamfanin gini. Suka ce mutumin ba ya zaune tare da iyalinsa, amma yana da maigadi da kuma mota a kori-kura guda daya. ‘’Ban taba ganinsa  tare da wani ba duk tsawon shekarun da ya yi a nan, kuma ba ya magana da kowa,’’ inji  wani makwabcin gidan.
Ya ci gaba da cewa, mun yi mamaki da muka ga sojoji sun mamaye yankin, kafin su afka cikin gidansa, mun kuma yi mamaki matuka da muka ga sun fito da mota shake da makamai.’’ Inji shi.
Wani makwabcin kuma cewa ya yi ,duk da cewa mazaunin wannan gidan ba  ya tare da iyalinsa, bai taba karbar bako ba kuma ba ya dadewa  bai dawo ba da dare.
Wata majiya daga jami’an tsaro ta ce ana bincike domin sanin ko makaman da aka gano suna da alaka da  masu tayar da kayar baya a wadansu sassan arewacin kasar nan. Duk da cewa suna da cikakkun shedun da ke nuna cewa masu makaman suna hulda da wani hamshakin dilllin makamai ne.
Aminiya ta gano cewa, an tafi da mazaunin gida tare da maigadinsa Abuja domin ci gaba da bincike, kuma ana binciken  wadansu mutane biyu ‘yan wadansu kasashen da ba a bayyana ba.