Rundunar JTF ta kame Fasto da buhun wiwi 124 a Maiduguri
Rundunar JTF mai aikin samar da tsaro a Jihar Borno ta ce bisa aiki da bayyanan sirri, jami’anta sun kame wani faston cocin Celestial Church of Christ da ke Maiduguri dauke da tabar wiwi buhu 124.Wata sanarwa dauke da sanya hannun kakakin Rundunar JTF Laftana Kanar Sagir Musa ya ce, jami’an sojojin sun kai farmaki […]
Rundunar JTF mai aikin samar da tsaro a Jihar Borno ta ce bisa aiki da bayyanan sirri, jami’anta sun kame wani faston cocin Celestial Church of Christ da ke Maiduguri dauke da tabar wiwi buhu 124.
Wata sanarwa dauke da sanya hannun kakakin Rundunar JTF Laftana Kanar Sagir Musa ya ce, jami’an sojojin sun kai farmaki cocin ne da misalin karfe 9:30 na safe a ranar 10 ga Yuli. “Bisa rahotannin sirri, JTF ta kai farmaki harabar cocin Celestial Church of Christ da ke Unguwar ’Yan Majalisa a yankin Pompomari da ke birnin Maiduguri. Farmakin ya jawo ganowa da kuma kame buhu 124 na wiwi da aka ajiye su a dakuna uku da ke harabar cocin. Wanda ake zargi mai suna Moses Edon ya yi ikirarin sanin abin da ke cikin buhunan, inda ya ce, wani mamban cocin mai suna Mista Segun Oni ne ya kawo tabar wiwin daga Jihar Ondo domin a adana masa,” inji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa, “Binciken farko ya gano cewa ba a gudanar da ayyukan bauta a cocin a baya-bayan nan. Ana amfani da shi ne a matsayin wurin hada-hadar kasuwancin wiwi, inda daga nan wasu ‘abokan hadin gwiwar kasuwanci” da ba a gano su ba, suka rarraba wiwin ga abokan cinikinsu a cikin Maiduguri da kewaye,” inji sanarwar.
Sai sanarwar ta tunara da jama’ar cewa akwai dangantaka a tsakanin miyagun kwayoyi da miyagun ayyuka da ke gudana a jihar. Domin haka ta bukaci daukacin al’ummar jihar su kai rahoton bayyanar miyagun kwayoyin ko dillalansu da ke tsakaninsu ga hukumomin tsaro.