Rundunar Juyin Juya-Hali ta Iran ta gargaxi Amurka kan jingina ta da ta’addanci
Wani babban Kwamandan Rundunar Juyin Juya-Hali na Iran Manjo Janar Mohammad Baqeri ya gargaxi Amurka cewa idan ta bayyana rundunar da ta ’yan ta’adda ko ta sake sanya musu sababbin takunkumi na iya jefa sojojinta da suke yankin a cikin haxari. Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ne ya ruwaito Janar Baqeri yana faxin haka kamar […]

Wani babban Kwamandan Rundunar Juyin Juya-Hali na Iran Manjo Janar Mohammad Baqeri ya gargaxi Amurka cewa idan ta bayyana rundunar da ta ’yan ta’adda ko ta sake sanya musu sababbin takunkumi na iya jefa sojojinta da suke yankin a cikin haxari.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ne ya ruwaito Janar Baqeri yana faxin haka kamar yadda ya samo daga kafar labarai ta rundunar mai suna Sepah News.
A farkon bana jami’an Amurka sun ce, Shugaba Donald Trump yana duba wata shawara da za ta ayyana wani vangare na rundunar juyin halin a matsayin qungiyar ’yan ta’adda.
Sannan a tsakiyar watan Yuni Majalisar Dattawan Amurka ta kaxa quri’a don sanya wa Iran sababbin takunkumi kan shirin makaman rokarta da sauran ayyukan da ba su shafi yarjejeniyar duniya da Amurka ta cimma da sauran manyan qasashin duniya kan Iran a shekarar 2015.
Sai dai wannan qudiri ba zai zama doka ba, sai Majalisar Wakilan Amurka ta amince kuma Shugaba Donald Trump ya sanya hannu a kai.
“Sanya Runduanr Juyin Juya-Hali a cikin qungiyoyin ta’addanci da sanya mata takunkumi wani babban haxari ne ga Amurka da sansanonin sojinta da ta tura yankin Tekun Fasha,” inji Manjo Janar Baqeri wanda shi ne Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Iran.
Sai dai bai yi bayani kan yadda wannan haxari da ya hango zai kasance ga sojojin Amurka da sansanoninta ba.
Sojin Rundunar Juyin Juya-Hali na Iran su ne rundunar tsaro mafi qarfi a Iran da suke sanya ido kan ximbin harkokin tattalin arzikin qasar tare da kula da biliyoyin Dala kuma suke da matuqar tasiri a harkokin siyasar qasar.
Janar Baqeri ya faxi a ranar Litinin cewa makaman roqa na Iran wani shiri ne na kare kai kuma ba za a sanya su a cikin abubuwan da za a tattauna ko sulhu a kai ba.
Sojojin rundunar dai suna yaqi a qasar Siriya domin fafatawa da qungiyoyin da suka yi ’yan tawaye ga Shugaba Bashar al-Assad.