Rundunar kwastam ta FOU ta kama tankar mai dauke da haramtattun kaji

Rundunar kwastam ta FOU ‘A’ Ikeja da ke Legas, ta yi nasarar kama daskararrun kaji da aka yi dabarar cunkusa su cikin wata babbar tankar man fetur domin badda-kama. kimar kajin ta kai fiye da Naira miliyan 13.Da yake nuna wa wakilan kungiyar masu kiwon kaji ta kasa da ’yan jarida kayan, sabon kwamandan rundunar […]

Rundunar kwastam ta FOU ta kama tankar mai dauke da haramtattun kaji
Rundunar kwastam ta FOU ta kama tankar mai dauke da haramtattun kaji

Rundunar kwastam ta FOU ‘A’ Ikeja da ke Legas, ta yi nasarar kama daskararrun kaji da aka yi dabarar cunkusa su cikin wata babbar tankar man fetur domin badda-kama. kimar kajin ta kai fiye da Naira miliyan 13.
Da yake nuna wa wakilan kungiyar masu kiwon kaji ta kasa da ’yan jarida kayan, sabon kwamandan rundunar ta FOU ‘A’, Kwanturola Nuhu Isa Mahmud ya ce, “A tarihin kafuwar rundunar ta FOU, ba a taba samun irin wannan sabuwar dabarar badda-kama ta masu fasa kwauri ba. Wannan babbar nasara ce a gare mu.”
Ya ce irin tashi-tsayen da Kwanturola-Janar Abdullahi Dikko Inde ya yi na kyautata wa jami’an kwastam ta fannonin wadata su da kayan aiki da biyansu albashi mai tsoka da ba su horaswa, a ciki da wajen Najeriya da kula da koshin lafiyarsu da iyalansu da makamantansu, ya taimaka wajen sadaukar da kan ma’aikatan wajen aikinsu.”
Kwanturola Nuhu ya jinjina wa hadaddiyar kungiyar masu kiwon kaji ta kasa kan kokarin da take yi wajen fafutukar yaki da shigowa da daskararrun kaji da talo-talo daga kasashen Turai. Ya ce zai yi iyakar kokarinsa wajen yakar ’yan sumoga a hurumin aikinsa na jihohi 6 a sashen Kudu maso Yamma da rundunar ta FOU ke kula da su.

… Ta jihohin Oyo da Osun ta lalata naman talo-talo mai dauke da guba

Kabir Yayo Ali, Daga Ibadan

Rundunar kwastam a jihohin Oyo da Osun ta bukaci jama’a da ke zaune a wannan sashe su dakatar da saye da kuma cin naman talo-talo da kaji da ake shigowa da su cikin kasa ta haramtacciyar hanya, domin mafi yawancin irin wannan kayan abinci suna da hadarin gaske ga rayuwar dan Adam a dalilin rubewar da suke yi tun kafin su shigo cikin kasa, sannan kuma,  ci gaba da amfani da su yana taimakawa wajen karya lagon kananan manoma na cikin gida bayan yi wa tattalin arziki zagon kasa.
Mataimakin kwanturola Muhammed Usman Bumba shi ne ya yi wannan kira a lokacin da ya jagoranci jami’ansa tare da ’yan jarida zuwa dajin da suka yi aikin lalata danyen naman talo-talo mai guba a cikinsa, wanda aka kama a cikin wata tirela da aka cunkusa katon-katon guda 19,750 a ciki da niyyar sayar wa bayin Allah.
Mataimakin kwanturolan ya ce jami’an kwastam sun yi nasarar kama wannan mota ne a ranar Asabar da ta wuce a kan tsohuwar hanyar Abeokuta zuwa Bakatari, bayan an kyankyasa musu labarin shirin shiga cikin birnin Ibadan dauke da wannan gurbataccen abinci da wasu ’yan sumoga suka yi.
Da yake yi wa ’yan jarida karin bayani, Mataimakin kwanturola Muhammed Bumba ya ce duk da yake ba su kama kowa a tare da haramtattun kayan ba, saboda sun gudu sun bar motar a tsaye ne, sai dai, “Mun gano irin dabarun badda-kama da aka yi ta hanyar shimfida kwanukan karfe guda dari 530 a kasa kafin a yi lodin danyen naman talo-talon a kansu tare da cunkusa buhuna masu dauke da dusar katako a gefen kayan da aka kiyasta jimlar kudinsu baki daya a kan Naira miliya 98 da dubu dari 6.” Inji shi.
Jami’in kwastam, DSC Alajogun Joseph, wanda ya jagoranci kamun wannan kaya, ya shaida wa ’yan jarida cewa kwanaki uku kafin ranar Asabar ne sun samu labarin kokarin shigowa da wadannan gurbatattun kayan abinci cikin kasar nan da suka yi kyakkyawan shirin kwanton-bauna da ya kai su ga cin nasarar kama kayan.