Rundunar kwastam ta kama harsashi dubu 30 a Jihar Oyo
Rundunar Kwastam a Jihohin Oyo da Osun ta kama harsashi dubu 30 a cikin katon 20 da aka yi dabarar dora buhunan garin alabo da doya a kan su domin badda-kama. An kama harsasan ne tare da direban motar a kan hanyar zuwa Ibadan daga garin Shaki. Mutum 2 da ake kyautata zaton su ne […]

Rundunar Kwastam a Jihohin Oyo da Osun ta kama harsashi dubu 30 a cikin katon 20 da aka yi dabarar dora buhunan garin alabo da doya a kan su domin badda-kama.
An kama harsasan ne tare da direban motar a kan hanyar zuwa Ibadan daga garin Shaki. Mutum 2 da ake kyautata zaton su ne suka mallaki kayan sun tsere a lokacin da jami’an kwastam suke binciken motar a tsakanin garin Shaki zuwa Ago Are a ranar Litinin.
Da yake nuna wa taron ‘yan jarida harsasan a ofishinsa, Kwamandan rundunar, Kwanturola Richard Oteri ya ce a cikin watan Mayu na bara ma, rundunar ta yi irin wannan nasara a lokacin da ta kama harsashi fiye da dubu 56, a wannan yanki na Shaki da ke kusa da kan iyakar Najeriya da kasar Benin.
Kwanturola Oteri ya jinjina wa Kwanturola Janar Abdullahi Inde Dikko saboda wadata rundunar da kayan aiki, musamman sababbin motoci kirar Hilud guda 3 da suka taimaka wajen karfafa wa jami’an guiwar gudanar da ayyukansu.
Da yake mika harsasan ga Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Oyo, Musa Kimo, Kwanturola Oteri ya ce ‘yan sanda ne za su ci gaba da yin binciken kwakwaf domin gano mutane 2 da suka mallaki harsasan da sauran binciken manufarsu.
Ya ce rundunarsa za ta ci gaba da yin aikin hadin guiwa a tsakaninta da sauran rundunonin tsaro a jihar domin maganin miyagun iri.
Direban motar kirar Toyota Hiace, mai lamba KW 286 SHH, mai suna Abdulraheem Adegoke ya shaida wa ‘yan jarida cewa bai san harsashi ne a cikin kwalayen da aka loda masa a cikin mota ba.
Ya ce mutane 2 (kabilun Ibo da Yoruba) da suka yi shatar motar tasa a kan Naira dubu 30 daga Shaki zuwa Ibadan ba su gaya masa gaskiyar irin kayan ba kafin su baro Shaki.