Rundunar Kwastam ta kama miyagun kwayoyi
Rundunar Kwastam shiyyar kudu maso yammacin Najeriya (FOU “A”) ta kama manyan sundukai guda 2 masu dauke da miyagun kwayoyin Tramadol dake sanya maye ga mashayansa da aka kiyasta kudin su a kan fiye da Naira miliyan 50 da aka shigo da su cikin kasa ba tare da izni ba. An yi satar shigo da […]
Rundunar Kwastam shiyyar kudu maso yammacin Najeriya (FOU “A”) ta kama manyan sundukai guda 2 masu dauke da miyagun kwayoyin Tramadol dake sanya maye ga mashayansa da aka kiyasta kudin su a kan fiye da Naira miliyan 50 da aka shigo da su cikin kasa ba tare da izni ba. An yi satar shigo da kwayoyin ne daga kasar Indiya kuma an kama mutane 15 da ake zargi da hannu cikin wannan al’amari.
Da yake mika kayan ga jami’an Hukumar kula da ingancin magunguna da kayan abinci (NAFDAC) a ranar laraba da ta wuce a ofishinsa a Legas, Kwamandan Rundunar, Kwanturola Muhammed Uba Garba ya ce “mun bayar da belin wasu daga cikin mutanen da aka kama kamar yadda doka ta tanadar domin doka bata ba mu iznin ci gaba da tsare su fiye da kwanaki 2 ba. Duka kayan kwayoyin mun mika su ga Hukumar NAFDAC da za ta gudanar da aikin lalata su bayan ta kammala bincike” inji shi. Mista Kinsley Ejeofor shi ne ya jagoranci karbar kwayoyin a madadin (NAFDAC).
Bincike ya tabbatar da cewa, ana sayar da irin wadannan kwayoyi na Tramadol a cikin kasuwanni da kantunan magani a sassa daban daban na kasa a inda matasa da manyan mutane da matan aure da masu ayyukan karfi suke saye suna sha. Wasu daga cikin mashaya irin wannan kwaya suna sha ne domin gusar da hankali a yayin da wasu suke amfani da kwayar domin kara kuzari.
Bayan mika kwayoyin ga Hukumar (NAFDAC) Kwanturola M.U. Garba ya nuna wa ‘yan jarida wasu daga cikin kayan da aka yi fasa kwaurin shigowa da su cikin kasa da rundunar tayi nasarar kama wa daga farkon watan jiya (Yuni) zuwa yanzu.Kayan sun hada da buhunan shinkafa da daskararrun naman kaji da sudaddun tayoyin mota da suturun gwanjo da takalma da man gyada da tumatirin gwangwani da sabulun wanka da wanki da kayan lantarki duka dake kunshe a cikin sundukai guda 7.
Kwanturola Garba ya ce, zai yi duk abun da yake iyawa musamman cikin dazuka da kan iyakoki da tashohin jiragen ruwa da filayen jiragen sama domin ganin ya dakile masu yin zagon kasa ga tattalin arzikin Najeriya da suke fitowa da sababbin dabaru wajen yin sumogan kayan da aka haramta shigowa da su cikin kasa. Sai dai ya ce, ba zai iya cimma burinsa ba said a taimakon kafofin labarai da sauran jama’a masu kishin kasa da son ci gabanta.