Rundunar Kwastam ta Ogun ta kama babura da kananan motoci dauke da shinkafa
Rundunar Kwastam a Jihar Ogun ta kama babura fiye da dubu daya dauke da buhunan shinkafa 4 zuwa 5 da masu sumoga suke amfani da su wajen biyan lada mai yawa ga matuka baburan domin dakon shigowa da haramtattun kayan daga jumhuriyar Benin.Da yake zagayawa da ’yan jarida don ganin kayan da suka kama a […]

Rundunar Kwastam a Jihar Ogun ta kama babura fiye da dubu daya dauke da buhunan shinkafa 4 zuwa 5 da masu sumoga suke amfani da su wajen biyan lada mai yawa ga matuka baburan domin dakon shigowa da haramtattun kayan daga jumhuriyar Benin.
Da yake zagayawa da ’yan jarida don ganin kayan da suka kama a ofishinsa da ke kan iyakar Idi-Iroko, Kwamandan rundunar, Kwanturola Mahmoud Haruna ya ce, “Mun kama baburan ne a cikin garin Idi-Iroko da cikin daji da suke yin jerin gwano, su fiye da 100 a lokaci daya, suna tseren shigowa da kayan, kuma kowanensu yana dauke da buhunan shinkafa 4 zuwa 5. Irin gudun da suke yi yakan haifar hadarin da kan kai su ga mutuwa da ko samun munanan raunuka, amma sai a rika dora alhakin hakan a kan jami’an kwastam, wadanda ke gudanar da ayyukansu. A sashen Abeokuta, kuwa masu fasa kwaurin suna yin amfani da manyan motocin tirela da kananan motoci wajen gudanar da danyen aikin nasu ne, a inda suke yin lodin buhu 70 zuwa 80 a cikin kowace karamar mota guda”.
Ya ce rundunar ta dauki tsauraran matakan dakile ’yan sumogar, sannan sukan bukaci sarakuna da dattijan gari da kungiyoyin masu motocin sufuri su taimaka wajen magance al’amarin. “Hukuma ba ta haramta sayen shinkafa da daga wata kasa domin shigowa da ita Najeriya ba, matukar za a shigo da su ta manyan jiragen ruwa ne a maimakon kan iyakokin kasa da ake amfani da motoci domin kin biyan kudin shiga”. Inji shi.
Kwanturola Mahmoud Haruna, ya nuna wasu mutum 3 da ya yi zargin sun kware wajen yin amfani da na’urorin bogi suna buga jabun takardun da suke karbar kudi daga hannun mutane da sunan takardar iznin shigowa da motoci cikin kasa.
Ya ce ’yan sanda da suke aiki tare suka kama su da jabun takardun kwastam da na bankuna da wasu na’urori da hatiman da suke yaudarar masu sayo motoci daga kasashen waje da takardun karya, alhali a kodayaushe suna tunatar da jama’a su gane irin illar bin miyagun hanyoyin shigowa da kaya cikin kasa.
Dangane da Kasuwar Duniya ta Free Trade Zone (FTZ) da ke kauyen Igbesa, a Jihar Ogun, Kwanturola Mahmoud ya yi na’am da yadda kamfanonin kasuwanci da masana’antu na ciki da wajen Najeriya suka rungume ta hannu biyu, a inda ta samar da guraben ayyuka dubu 2 da 500 ga ’yan Najeriya.