Rundunar OPSH ta yi aikin tsabtace muhalli a Jos
Jami’an Rundunar Tabbatar da Zaman Lafiya da Tsaro a Jihar Filato (OPSH) sun gudanar da ayyukan tsabtace muhalli a garin Jos da ke jihar. Aikin wanda aka gudanar da shi a ranar Litinin da ta gabata an yi shi ne tun daga shataletalen Asibitin Filato zuwa Shataletalen Old Airport Junction har zuwa Unguwar Rayfield da […]
Jami’an Rundunar OPSH a yayin da suke aikin tsabtace muhalli a Jos
Jami’an Rundunar Tabbatar da Zaman Lafiya da Tsaro a Jihar Filato (OPSH) sun gudanar da ayyukan tsabtace muhalli a garin Jos da ke jihar.
Aikin wanda aka gudanar da shi a ranar Litinin da ta gabata an yi shi ne tun daga shataletalen Asibitin Filato zuwa Shataletalen Old Airport Junction har zuwa Unguwar Rayfield da ke Jos babban birnin jihar.
Aminiya ta gano an fara gudanar da aikin ne daga karfe 7: 00 na safe zuwa 11 na safe a karkashin jagorancin Shugaban Ma’aikata na Rundunar, Birgediya Janar Mohammed Bello.
A lokacin da Birgediya Janar Bello yake tattaunawa da ’yan jarida ya bayyana cewa, wannan aikin yana daya daga cikin aikace-aikacen da ba na nuna karfi ba da rundunar take gudanarwar don tabbatar da dorewar zaman lafiya a Jihar Filato.
Ya ce, “Kamar yadda kuka sani ne, muna gudanar aikace-aikace makamantan haka duk don zaman lafiya ya samu dorewa a Filato, to wannan aikin tsabtace muhallin da muke yi yana daya daga cikin wadannan aikace-aikace da ba na nuna karfi ba duk don zaman lafiya ya samu dorewa.”
Janar Bello ya ce babban makasudin shirya wannan aikin shi ne don a kara samun fahimtar juna a tsakanin Rundunar OPSH da kuma jama’ar jihar.
Ya ce, “Rundunarmu za ta ci gaba da gudanar da wannan aiki lokaci zuwa lokaci, kuma za mu ci gaba da yi don mu samu amincewar jama’a su fahimci ba mu da wani buri face a samu zaman lafiya a jihar.”
A karshe ya bukaci jama’a su ci gaba da ba jami’an rundunarsu hadin kai don su ci gaba da sauke nauyin da ke kansu ba tare da wata cikas ba.