Taoreed Lagbaja: Shin Shugaban Sojin Ƙasan Najeriya ya mutu?

Hedikwatar Sojin Ƙasa ta Nijeriya ta ƙaryata labarin mutuwar Babban Hafsan Rundunar, Laftanar-Janar Taoreed Lagabja

Taoreed Lagbaja: Shin Shugaban Sojin Ƙasan Najeriya ya mutu?

Hedikwatar Sojin Ƙasa ta Nijeriya ta ƙaryata labarin da ke yawo cewa Babban Hafsan Rundunar, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja, ya mutu.

Rundunar ta ce babu kamshin gaskiya a labarin mutuwa ko rashin lafiyarsa, inda ta bayyana cewa Janar Taoreed Lagbaja ya tafi hutun aiki ne.

Sanarwar da kakakin rundunar, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, ya fitar ta bayyana cewa kafin tafiyar Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja hutu, sai da ya damƙa ragamar jagorancin  rundunar a hannun Daraktan Dokoki da Tsare-tsare, Manjo-Janar Ibrahim Bagudu Abdulsalam.

Ya bayyana cewa a halin yanzu, Manjo-Janar Ibrahim Bagudu Abdulsalam shi ne Muƙaddashin Babban Hafsan Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya kuma yana gudanar komai yadda ya kamata.

Onyema Nwachukwu ya ci gaba da cewa, rundunar da sauran rundunonin tsaron Najeriya suna da kyakkyawan tsarin gudanarwq da shugabanci domin tabbatar da komai na tafiya daidai idan wanda ke kan wata kujera ya yi tafiya ko idan ta Allah ta kasance.

Ya ƙara da cewa, don haka, babu wani giɓi a shugabanci da tafiyar Janar Lagabja ta haifar a rundunar kamar yadda labarin ƙanzon kuregen ke cewa.

Rundunar ta fitar da sanarwar ce bayan labari ya karaɗe kafofin sada zumunta cewa Janar Taoreed Lagbaja ya rasu a ƙasar waje sakamakon cutar daji.

Labarin ya riya cewa Janar Lagabja ya jima da mutuwa amma rundunar ba ta sanar ba a hukumance, saboda kamun ƙafa da wasu manyan hafsoshi a rundunar suke yi domin maye gurbinsa.

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano