Rundunar Sojin Najeriya ta yi ƙarin haske kan fargabar juyin mulki
Akwai masu kiraye-kirayen juyin mulki saboda matsalar tsaro da tsadar rayuwa da ake fuskanta.
Rundunar Sojin Kasa ta Nijeriya ta yi ƙarin haske game da fargabar juyin mulki da ake raɗe-raɗi a sassan ƙasar.
A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta ce dakarunta ba su da wata aniyya ta karɓe ragamar iko daga tsarin mulkin dimokuraɗiyya, tana mai cewa “tsarin dimokuraɗiyya zama daram.”
Babban Hafsan Sojin Kasa na Nijeriya, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja ne ya bayyana hakan a cikin maƙalar da ya gabatar yayin wata laccar da rundunar ta gudanar a Hedikwatar Tsaro ta Kasa da ke Abuja.
Lagbaja ya jaddada cewa rundunar sojin Nijeriya za ta ci gaba da kare Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya, haka kuma, ba za ta sauya wannan akida ba ko tunanin kawo wa tsarin wata tangarda ba saboda wani dalili.
A cewar babban hafsan, sojojin Najeriya za su ci gaba da kasancewa jakadun dimokuraɗiyya, “yayin da riƙo da akalar jagoranci ya rataya a wuyan shugabanninmu da muka zaba su yi jagoranci mu kuma sojoji ke gudanar da namu aikin kamar yadda kundin tsarin mulkinmu ya tanada.”
Ya kuma bukaci sojojin Najeriya da su kasance masu ƙwazo da kwarewa sannan su mayar da hankali wajen gudanar da ayyukansu bisa tsarin mulki.
A bayan nan ne rundunar sojin Najeriya ta gargadi masu kiraye-kirayen juyin mulki, sakamakon matsalar tsaro da kuma tsadar rayuwa da ake fuskanta a faɗin kasar nan.
Najeriya dai na fuskantar matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa mafi muni a tarihi, abin da ya haifar da zanga-zanga a wasu sassan ƙasar nan.
Wasu daga cikin ’yan kasar sun jima suna kiraye-kirayen sojoji su kifar da gwamnatin dimokuraɗiyya domin karɓe iko kamar yadda aka yi a Jamhuriyar Nijar.
Sai dai Daraktan Tsaro na Sojin Najeriya, Janar Christoper Musa, ya ce masu wannan kiraye-kiraye ba sa nufin kasar da alheri.
Dangane da wannan batu ne Janar Musa ya ce dakarun sojin Najeriya za su sa kafar wando ɗaya da masu wannan kiraye-kirayen.
Ya ce abin da sojoji za su yi a yanzu shi ne kawai duba hanyoyin samar da sauƙi da kuma ciyar da kasar gaba, amma ba maganar juyin mulki ba.
Da yake tabbatar da halin matsi da ’yan Nijeriya ke ciki, Janar Musa ya ce babu inda juyin mulki ke zama alheri a duniya don haka ba za su yi wa Nijeriya fatan koma bayan da yake biyo bayan juyin mulki ba.
Ya bukaci ’yan Najeriya da su kara haƙuri kan halin da kasar ke ciki a yayin da mahukunta ke ci gaba da ƙoƙarin an samu sauƙin al’amura a ƙasar.