…Rundunar sojin kasar na so a gudanar da zabe

Wata majiya a Zimbabwe ta sanar da Jaridar Independent cewa rundunar sojin na kokarin ganin yadda za a samu damar gudanar da zabe a kasar. Ita dai rundunar sojin ta doge a kan cewa ba juyin mulki ta yi ba. Kawai dai suna neman wasu daga cikin jami’an gwamnatin Mugabe ne, amma shi Mugabe yana […]

…Rundunar sojin kasar na so a gudanar da zabe

Wata majiya a Zimbabwe ta sanar da Jaridar Independent cewa rundunar sojin na kokarin ganin yadda za a samu damar gudanar da zabe a kasar.

Ita dai rundunar sojin ta doge a kan cewa ba juyin mulki ta yi ba. Kawai dai suna neman wasu daga cikin jami’an gwamnatin Mugabe ne, amma shi Mugabe yana cikin koshin lafiya, kuma yana karkashin kulawarsu.

Shi ma Shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zouma, ya tabbatar da cewa Shugaba Mugabe ya tabbatar masa ta wayar tarho cewa yana cikin koshin lafiya.

Da alamu cewa tsohon mataimakin Shugaban kasar, Mista Mnangagwa wanda ya tsere zuwa Afirka ta Kudu a makon da ya ganata ne sojin kasar ke so ya ci gaba da jan ragamar kasar. Sannan kuma akwai yiwuway tsohon shugaban ‘yan adawan, Mista Tsbangirai ya zama mataimakin shugaban kasar. Morgan Tsbangirai wanda shi ne shugaban adawa a kasar ya dawo bayan an fara wannan dambarwar.

Morgan dai ya dade yana takun saka da Shugaba Mugabe, wanda hakan ya yi sanadiyar kama shi saboda yana yawan magana a kan gwamnatin Mugabe.

An taba kama shi a shekarar 2000, inda aka zarge shi da cin amanar kasa, sannan kuma aka zarge shi da shirya yadda za a kashe shugaba Mugabe a shekarar 2002 sannan daga baya aka sake shi bayan ya samu nasara a kotu.

Morgan ya taba rike Firaministan kasar daga shekarar 2009 zuwa 2013, bayan ya amince ya yi gwamnatin hadaka da Shugaba Mugabe. 

Tsohon Firaministan dai ya taba tsayawa takarar shugabancin kasar a shekarar 2008, inda ya samu kuri’u kashi 47.8, inda ya wuce Mugabe wanda ya samu kuri’u 43.2, amma daga bisani sai ya janye a zagaye na biyu na zaben, idan ya ce ya san ba za a yi zabe mai nagarta ba.