Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansaninta a Kebbi
Rundunar ta ziyarci Kebbi ne domin duba yadda za ta samar da sansaninta a jihar.
Rundunar sojin ruwan Najeriya ta bayyana aniyar kafa sansaninta a Ƙaramar Hukumar Yauri ta Jihar Kebbi a wani mataki don bunƙasa harkokin tsaron iyakokin ruwa.
Hakan na zuwa ne bayan da wata tawagar manyan jami’an sojojin ruwan suka kai ziyara gidan gwamnatin Jihar Kebbi.
Sojojin sun kai ziayarar ne ƙarƙashin jagorancin Rear Admiral Patrick Nwatu – wanda ya wakilci babban hafsan sojin ruwan ƙasar.
Rundunar ta ziyarci Kebbi ne domin duba yadda za ta samar da sansaninta a jihar.
Patrick Nwatu ya yi tir da harin ta’addanci a kogin Neja, yana mai cewa yankin ya zama maɓoyar masu safarar makamai da sauran masu aikata laifuka.
Rundunar sojin ruwan Najeriya ta ce ta kammala shirye-shiryen kafa sansanin sojin ruwa a garin Yauri da ke jihar.
Babban Hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla ne ya bayyana hakan a wata ziyarar ban girma da suka kaiwa Gwamnan Kebbi, Nasir Idris a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi a ranar Alhamis.
Da yake jawabi yayin ziyarar, jagoran tawagar Rear Admiral Patrick Nwatu, ya ce ziyarar wani ɓangare ne na faɗaɗa dabarun teku na sojojin ruwan Najeriya.