Rundunar STF ta kubutar da mutum 8 daga masu satar mutane
Jami’an Rundunar Tsaro ta Musamman (STF) mai aikin samar da zaman lafiya a Jihar Filato sun damke wasu mutane da ake zargi da satar mutane a garin Jos babban birnin Jihar Filato, inda suka kubutar da mutum 8 daga hannunsu. Wata sanarwa da ta fito daga rundunar dauke da sanya hannun kakakinta Kyaftin Salihu Ibrahim […]
Jami’an Rundunar Tsaro ta Musamman (STF) mai aikin samar da zaman lafiya a Jihar Filato sun damke wasu mutane da ake zargi da satar mutane a garin Jos babban birnin Jihar Filato, inda suka kubutar da mutum 8 daga hannunsu. Wata sanarwa da ta fito daga rundunar dauke da sanya hannun kakakinta Kyaftin Salihu Ibrahim Mustapha ce ta bayyana haka.
Rundunar ta ce sakamakon rahoton sirri da ta samu, jami’anta sun kai samame a wani otel da ke Unguwar Zinariya a garin Jos mai suna Chiwarna inda suka damke wadanda ake zargin tare da kubutar da wasu mutum 8 da suka sace.
Sanarwar rundunar ta ce a binciken da jami’anta suka yi kan wannan al’amari, sun gane cewa wadanda ake zargi da satar mutanen, sun sato ne daga wurare daban-daban a cikin garin Jos suka zo suka kulle su a wannan otel.
Rundunar ta yi bayanin cewa barayin mutanen sun fara tuntubar iyalan wadanda suka sace, domin su karbi kudin fansa kafin su sake su.
Sanarwar ta ce jami’an rundunar sun kama jagororin masu satar mutanen tare da manajan otel din, kuma jami’an rundunar suna ci gaba da bincike kan al’amarin.