Rundunar STF ta kwato shanu 150 da aka sace a Wase
Rundunar tsaro ta musamman da ke aikin samar da zaman lafiya a Jihar Filato (STF) ta tarwatsa wasu barayin shanu tare da kwato shanu 150 da suka sace a yankin Mabo da ke karamar Hukumar Wase a jihar a ranar Juma’ar da ta gabata.Wata sanarwa da ta fito daga rundunar dauke da sanya hannun Kakakinta […]
Rundunar tsaro ta musamman da ke aikin samar da zaman lafiya a Jihar Filato (STF) ta tarwatsa wasu barayin shanu tare da kwato shanu 150 da suka sace a yankin Mabo da ke karamar Hukumar Wase a jihar a ranar Juma’ar da ta gabata.
Wata sanarwa da ta fito daga rundunar dauke da sanya hannun Kakakinta Kyaftin Salihu Mustafa ta ce a ranar Juma’ar da ta gabata da misalin karfe 3:30 na dare, wasu mutane da ba a gane ko su wane ne ba, sun sace shanu 150 a yankin Mabo da ke karamar Hukumar Wase a Jihar Filato.
Sanarwar ta ce a lokacin da jami’an rundunar suka samu rahoton faruwar al’amarin, nan take suka isa dajin da al’amarin ya faru suka zagaye shi.
Ta ce da barayin shanun suka ga jami’an tsaron nan take suka gudu suka bar shanun suka shiga daji. Sanarwar ta ce tuni jami’an rundunar suka mika shanun ga masu su.
Rundunar ta nuna takaici kan yawaitar sace-sacen shanu a yankin, musamman a wannan lokaci da ake kokarin ganin a samu zaman lafiya a jihar, sai ta gargadi masu yin zagon-kasa ga kokarin da ake yi na samun zaman lafiya a jihar da su guji yin haka.