Rundunar tsaro ta jibge gawarwaki 3,335 a asibitin Borno – Rahoto

Gawarwaki 3,335 ne sojoji suka jibge a asibiti daya a Jihar Borno a cikin wata shida a bana, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Associate Press (AP) ya bayar da rahoto. Kamfanin AP ya fadi a cikin rahoton cewa adadin na kunshe ne a wani jerin sunaye na asibitin da ya ci karo da su.Rahoton […]

Rundunar tsaro ta jibge gawarwaki 3,335 a asibitin Borno – Rahoto

Alhaji Sambo Dasuki Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan TsaroGawarwaki 3,335 ne sojoji suka jibge a asibiti daya a Jihar Borno a cikin wata shida a bana, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Associate Press (AP) ya bayar da rahoto. Kamfanin AP ya fadi a cikin rahoton cewa adadin na kunshe ne a wani jerin sunaye na asibitin da ya ci karo da su.
Rahoton ya zo ne kwanakin kadan da kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Duniya (Amnesty International) ta saki wani rahoto da ya ce, mutum 950 sun mutu lokacin da suke tsare a hannu sojoji cikin wata shida na farkon bana. Sai dai Aminiya ba ta samu jin ta bakin Daraktan Labarai na Hedkwatar Soja, Birgediya Janar Chris Olukolade kan lamarin ba.
A rahoton AP ya ce bayanan dakin ajiye gawa na wani asibiti daya ya nuna yawan wadanda suka mutu a lokacin da suke tsare a hannun sojoji ya ninka sau uku a watan Yuni, wata na farko na dokar ta-bacin a yankin Arewa maso Gabas, lamarin da ke nuna fadadar yaki da masu dauke da makamai.
Bayanan da Kamfanin AP ya samu na wata tara da ya fara daga 5 ga Oktoban bara zuwa 5 ga Yulin bana, ya nuna sojoji sun kashe dubban mutane a yunkurinsu na murkushe ’yan Boko Haram din. Bayanin ya fito ne daga asibiti daya kacal, wato Asibitin Koyarwa na Maiduguri, cibiyar kungiyar Boko Haram.
A cikin kwana 30 kafin kafa dokar ta-baci a ranar 14 ga Mayu, sojoji sun kai gawarwaki 380 zuwa asibitin, amma bayan kwana 30 da kafa dokar adadin ya koma 1,321. Sannan a watan Yuni adadin ya koma 1,795, inda ya zama watan da sojojin suka fi kai gawarwakin mutanen da aka halaka zuwa asibitin cikin motocin daukar gawa da ke samun rakiyar motocin yaki. Wannan adadi ya zarce na daukacin mayakan Boko Haram da aka kiyasta.
Rahoton ya ce, gwamnatin Najeriya da mahukuntan sojan kasar nan sun ki cewa uffan kan lamarin, kuma abu ne mawuyaci a gano matattu nawa daga cikinsu suke da alaka da Boko Haram. Kuma dokokin Najeriya sun ce koda a karkashin dokar ta-baci, wajibi ne a gabatar da wadanda aka kama a gaban Kotun Majistare cikin awa 48, kuma a ba su damar ganawa da lauyoyi da iyalansu.
Wani fasto ya ce an tsare shi a Barikin Soja na Giwa da ke Maiduguri bayan an kama shi tare da wasu mutum hudu saboda an samu makamai boye a wani kamfanin takalma da suke aiki. Ya bayyana yadda aka cusa daruruwan mutanen da aka yi musu tsarara a wani sel da aka yi shi domin ’yan mutane kadan. Ya ce sau daya a yini soja ke jefa ledar burodi daya cikin sel din inda mutanen za su rika wawaso. Kuma wasu suna mutuwa saboda gallazawa.
Ya shaida wa AP cewa an sake shi ne sakamakon sanya bakin wata kungiyar Kiristoci da yadda wadanda suka tsare shi suka gane addu’arsa ta samun ceto a matsayin Kirista. Faston ya nemi a sakaya sunansa saboda tsoron daukar fansa daga sojojin.  
A makon jiya kungiyar Amnesty ta ruwaito cewa daruruwan mutanen da aka tsare na mutuwa a hannun sojoji: wasu ana fitar da su ne daga sel a je a harbe, wasu kuma suna macewa ne saboda cunkoso ko yunwa.
kungiyar mai matsguni a Landan ta ce, “labari mai tushe,” daga wani babban sojan Najeriya ya nuna sojoji sun kashe mutanen da suke tsare da su har 950 a wata shida na farkon bana. Sannan ga bayanan dakin ajiye gawarwakin da AP ya ga sunan mutum 3,335 a tsakanin wannan lokaci a asibiti daya kacal. Wannan adadi ya ninka fararen hula 400 da ’yan Boko Haram suka kashe a hare-harensu a wannan tsakani har sau tara, kamar yadda AP ya ruwaito.
Sai dai su ma ’yan Boko Haram sun dada jawo wa kansu bakin jini a wurin jama’a, sakamakon yadda mayakansu suka rika harbe daliban makaranta, wasu ma a lokacin da suke rubuta jarrabawa, kuma suka rika banka wuta ga wasu daliban da ransu a wata makarantar kwana.
kungiyar Boko Haramdai ta fi kashe Musulmi fiye da Kirsitoci, inda a watan Agustan da ya gabata ta bindige masallata 47 a wani masallaci. Sannan a watan jiya sun yi garkuwa da ladanin wani masallaci suka tilasta shi kiran Sallah da asuba, inda suka kashe wasu dattawa bakwai da suka fara zuwa masallacin bayan jin kiran Sallar.
kungiyoyin kare hakkin dan Adam na ciki da wajen kasar nan, sun ce sojojin da aka tura domin murkushe ’yan Boko Haram suna wuce gona da iri yayin aikinsu, inda suke fadawa gidajen jama’a su kai hari ko su tsare mutane bisa zalunci.
kasashen Yamma na jingina tashin hankali da rikicin addini da ke aukuwa a Arewa kan karuwar talauci da danniyar da ake nuna wa al’ummar yankin Musulmi da Kirista. Kwanaki kadan da kafa dokar ta-bacin Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry ya “nuna tsananin damuwa kan mugun cin zarafi da jami’an tsaron Najeriya ke yi ga jama’a.” Kuma a watan Satumban da ya gabata Shugaba Jonathan da takwaransa na Amurka Barack Obama sun tattauna batun yaki da ta’addanci ta hanyar samar da wani gamammen shirin da zai bullo da hanyoyin inganta tattalin arziki ga jama’a da kuma kare hakkin dan Adam, kamar yadda sashin harkokin cikin gida na Amurka ya nuna.