Rundunar ’yan sanda ta gindaya wa masu shirya zanga-zanga sharuɗa
Rundunar ’yan sanda ta ce an ɗauko sojojin haya daga ƙasashen ƙetare a shirye-shiryen shiga zanga-zanga.
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta buƙaci masu shirya zanga-zangar matsin rayuwa a faɗin ƙasar da su miƙa mata bayanansu.
Babban Sufeton ’yan sandan Nijeriya Kayode Egbetokun ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai ranar Juma’a a Abuja.
- Gwamnati ta soma ɗaukar mataki kan fim ɗin wulaƙanta Hijabi
- Shugaban Gabon ya gayyaci Dangote ya kafa masana’antun taki da siminti a kasarsa
Kayode Egbetokun wanda ya tabbatar da cewa ’yan kasa na da cikakken ’yancin gudanar da zanga-zanga ta lumana, ya kuma shawarci masu shirya ta da su sake tunani gabanin farawa.
Egbetokun ya ce duk masu shirya zanga-zangar ko ɗaukar nauyi su miƙa wa kwamishinonin ’yan sandan jihohinsu sunayensu da adireshi domin hakan zai tabbatar da cewa an yi zanga-zangar cikin lumana.
Sauran sharuɗan da babban jami’in ’yan sandan ya gindaya sun haɗa da miƙa wa rundunar bayanan hanyoyin da za a bi yayin gudanar da zanga-zangar da kuma wurin haɗuwa da kuma tsawon lokacin da zanga-zangar za ta ɗauka.
Kazalika, Babban Sufeton ’yan sandan ya ce rahotannin sirri sun tabbatar musu an ɗauko sojojin haya daga ƙasashen ƙetare a shirye-shiryen shiga zanga-zangar.
Sai dai shugaban ’yan sandan bai yi wani ƙarin bayani kan zargin shigowar sojojin hayar ƙasashen ƙetare ba cikin zanga-zangar.
“Muna bibiyar yadda lamura ke faruwa kan zanga-zangar da take mana barazana, yayin da wasu ƙungiyoyi ke neman a yi zanga-zangar tashin hankali irin ta Kenya, wasu kuma na kira a kwantar da hankali a yi ta cikin nutsuwa ba tashin hankali.
“Wasu na kiran a yi zanga-zangar nutsuwa amma da kausasan kalamai, wani abu da yake sa mu nazari kan gaskiyar lamarinsu.
“Muna da tarihin zanga-zangar da aka yi ta rikici a Najeriya. A ganina ya kamata mu kalli wasu zanga-zangar da ake yi a wasu ƙasashen da suka zama masu haɗari.
“Muna kira ga ’yan Najeriya masu kishin ƙasa da su janye daga wannan zanga-zanga, saboda illar da ke cikinta da ta fito ƙarara da kuma rashin sani ga matasan da suke kira a yi tashin hankali,” in ji Egbetokun.
Aminiya ta ruwaito cewa, an shirya zanga-zanga a faɗin ƙasar daga 1 ga watan Agusta zuwa 10 saboda tsadar rayuwa.