Rundunar ‘yan sandan jihohi

Ba ma sai an fada ba Najeriya na fama da matsalolin tsaro a wannan marrar  wadanda  ba ta taba fuskantar  irinsu ba tun bayan da aka kammala yakin basasa  a shekarar 1970. An sha yin batutuwa da tarurruka game da yadda za a inganta aikin ‘yan sanda da kuma hanyoyin  kyautata al’amuran da suka jibanci […]

Rundunar ‘yan sandan jihohi

Ba ma sai an fada ba Najeriya na fama da matsalolin tsaro a wannan marrar  wadanda  ba ta taba fuskantar  irinsu ba tun bayan da aka kammala yakin basasa  a shekarar 1970. An sha yin batutuwa da tarurruka game da yadda za a inganta aikin ‘yan sanda da kuma hanyoyin  kyautata al’amuran da suka jibanci tsaro, amma an kasa shawo kansu yadda ya kamata. An kakkafa kwamitoci da yawa game da haka, an kuma firfitar da rahotanni masu armashi da gamsarwa dangane da wannan batu don dai a samar da  rundunar ‘yan sandar da za ta yi aiki daidai da yadda kundin tsarin mulki ya kayyade.

Wani tsohon Kwamishinan ‘Yan Sanda, Abubakar Tsab, wanda ya yi aiki da wani kwamitin  gyara ga aikin dan Sanda,  ya ce kodayake shi ba shi da ra’ayin kirkiro rundunar ‘yan sandan jihohi, amma rashin biyan bukatar da ake samu game da yanayin aikin dan Sanda a halin yanzu ya sa ya fara tunanin kago wata dabarar da za ta kai ga magance haka. To, an sha yin tarurruka game da wannan batu, kuma har gobe ana nan ana neman mafita daga matsalolin da ke hana rundunar ‘yan sandan Najeriya biyan kwakkwarar bukata game da dalilan da suka sanya aka kafa ta. 

kwararrun jami’an tsaro na ta wasa bakunansu game da hujjojin amincewa da kafa rundunar ‘yan sandan jihohi da kuma dalilan da suke gani  sun  haramta yin haka. Ko a Majalisar Dattijai ma an taba tabo wannan batun  sa’ilin da ake kokarin yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin 1999, a shekarar 2010. An nemi a gano hanya mafi dacewa ta sarrafa rundunar ‘yan sandan kasar nan don tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyar al’umma.

Babu wani abin da wadanda suka kosa su ga an kafa rundunar ‘yan sandan jihohi ke jira kamar amincewa da dokar da za ta bayar da damar yin haka da kuma samar da kayayyakin aiki na zamani da horar da wadanda za su yi aiki da su. To amma ai  kodayake sai jami’an tsaron da  doka ta san da zamansu ne kawai za su yi aikin tsaro, su kuma dauki makamai,  wasu gwamnatocin jihohi sun kirkiro rundunonin tsaro masu kama da na ‘yan sanda, wadanda ba su daukar makamai,  tun daga lokacin da aka mayar da mulki hannun farar hula a shekrar 1999. Sa’ilin da ayyukan ta’adanci kamar su fashi da makami da satar bil-adama da shiga gidajen mutane suka yawaita a shiyyar Kudu-maso-Gabas, sai gwamnatocin jihohin Abia da Anambra suka kakkafa kungiyoyin ‘yan banga , watau  bigilante groups wadanda ake kira Bakassi Boys.

Haka nan kuma sa’ilin da Malam Ibrahim Shekarau  ya mulki Jihar Kano na tsawon shekaru takwas ya nemi ya kyautata halayyar jama’arsa ta hanyar daidaita sahun al’amuransu  da kuma cusa masu da’a da tsoron Allah a dukkan ayyukansu,  Dangane da haka ne ya kafa Hukumar Hisba, wacce ma’aikatanta da suka kasance tamkar sojoji, suka dage wajen ganin ana aiki da dokoki da ka’idojin da suka dace da abin da jama’ar jihar suka yi imani da shi watau addinin Islama. Takwaransa na Jihar Barno a wancan lokacin, Ali Modu Sheriff, ya nemi tattake abokan adawar siyasarsa, wadanda yake gani tamkar ba su da ‘yancin walwala da walawa a siyasance a jihar, sai kawai  ya bullo da wata kungiyar da ake kira ECOMOG  wacce ta yi maganinsu, ta kuma hana su sakat, har sai da suka bi, suka kuma mika wuya.

Sa’ilin da ake ganin cewa Bakassi Boys a jihohin Abia da Anambra suna taimaka wa ‘yan sandan gwamnatin tarayya a farkon kafuwarsu wajen rage yawan aikata masha’a, amma sai cikin dan kankanen lokaci suka  zame karnukan farautar gwamnonin jihohinsu, ana ta cinna wa wadanda gwamnonin ke gani makiyansu ne a zahiri da badini.  Muhimman ayyukan da wadannan kungiyoyin tsaron da gwamnatocin jihohi suka kakkafa  suka fi mayar da hankulansu akai su ne tsarewa da wahalar  wadanda aka zarga da aikata laifuffuka,  wani sa’in ma har kisan kai sukan aikta a sakamakon haka, ko kuma idan an gamu da karar kwana. Wannan ne ya sa gwamnatin tarayya ta sossoke su, duk kuwa da cewa wasunsu dokar majalisun jihohinsu ne suka samar da su. 

Amma duk da haka nan kungiyar Gwamnonin Najeriya sun sha kokartawa wajen kiraye-kirayen  ba su damar kakkafa rundunonin ‘yan sanda  na jihohi, saboda ganin cewa yin haka zai taimaka wajen  inganta nauyin da gwamnatocin jihohi ke dauka  wajen gudanar da harkokin tsaro a jihohinsu. Amma daga bisani sai wasu gwamnonin, musamman na Arewa suka fara nuna adawa da wannan batu na rundunar ‘yan sandan jihohi a wancan lokacin, domin guda 18 daga cikinsu sun sake tunanin kan al’amarin sun kuma janye ra’ayoyinsu game da haka. A maimakon haka nan sai Gwamnonin Arewa suka ce ya kamata gwamnatin tarayya ta kara inganta  rundunar ‘yan sandan Najeriya  don hakan ya biya bukata yadda ake so.

A game da haka an gano cewa  shawarwarin da aka sha bayarwa  a tarurrukan da aka sha yi don yin gyararrakin da za su inganta  rundunar ‘yan sanda  ba za a iya aiki da su ba  muddin dai ba gyara  kundin tsarin mulki aka yi ba don a sanya su a ciki. Shi ya sa  gwamnonin jihohi na wannan marrar ke so  lallai sai an yi gyara ga sassa na 214 da kuma na 215 na kundin tsarin mulkin 1999 don  a ji dadin kafa rundunonin ‘yan sandan jihohi. Kodayake akwai jama’a da yawa da ke goyon bayan gwamnonin da ke kira a kakkafa rundunonin ‘yan sandan jihohi, alhali kuma ba su  so a sake fasalta tsarin gudanar da al’amurran kasar nan don a ji dadin yin hakan, amma sai dai ana tsoron cewa gwamnonin jihohi ba za su yi amfani da ‘yan sandan jihohi ba ta hanyoyin da suka dace, za su yi ne kawai don biyan bukatunsu na kashin  kansu.

Babu inke ko wai game da  wannan hasashe, domin kuwa gwamnonin za su so su ci moriyar ‘yan sandan da suke biya da kudin gwamnatocin jihohinsu, kuma hakan zai ba su damar yin amfani da su wajen takurawa da muzgunawa abokan adawa ko masu hamayya da su a siyasance, musamman a lokutan zabe. Yanzu ma yaya lafiyar kura balle ta yi hauka? Ai an ga yadda gwamnonin jihohi ke karkata akalar hukumomin zabe na jihohinsu wajen cinye  dukkan kujerun zaben kananan hukumomin jihohinsu, su bar ‘yan adawa suna kukan banza. To amma hakan zai sa a ki kirkiro rundunonin ‘yan sandan jihohi, ganin cewa  Majalisar Dattijai da ta dade tana neman a yi haka ta watsar da batun yanzu ? Oho! Watakila sai  ranar da jaki ya yi kaho.

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos