Rundunar ‘Yan Sandan Kuros Riba ta kwato makamai 324
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kuros Riba ta ce ta kwato makamai 325 daga hannun wasu bata gari dake sassan jihar. Da yake gabatar da dimbin makaman ga manema labarai, a harabar ofishinsa, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Hafiz Muhammad Inuwa ya ce sun samu wannan nasara ce a yayin wasu samame da rundunar ta rika kai […]
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kuros Riba ta ce ta kwato makamai 325 daga hannun wasu bata gari dake sassan jihar. Da yake gabatar da dimbin makaman ga manema labarai, a harabar ofishinsa, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Hafiz Muhammad Inuwa ya ce sun samu wannan nasara ce a yayin wasu samame da rundunar ta rika kai wa maboyar tasu da ake kyankyasa mata.
Kwamishinan ya ci gaba cewa rundunar ma ta yi sa’ar cafke wasu da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka hada da fyade cikin su akwai ma wanda ya yi wa wata karamar yarinya ‘yar shekara 9 da haihuwa da kuma hada baki wajen yin zamba cikin aminci da fashi da makami da sauran ayyuka na ta’adanci, har mutum 78.
Hafiz Muhammad Inuwa ya kara da cewa daga cikin wadanda aka kama akwai wanda aka kama shi yana zambatar rundunar tsaro ta farin kaya wato Sibil Difens da ta ‘yan sanda, yana karbar kudade hannun jama’a yana cewa za a dauke su aiki. Sai kuma Kwamishinan ‘yan sandan ya gargadi al’ummar jihar da duk wani wanda ya san yana ajiye ko rike da makami ba bisa ka’ida ba ya mutunta kansa cikin ruwan sanyi ya mika makaminsa kafin doka ta yi aiki a kansa.
Rundunar ta kafa kwamitin mutum shida da za su yi aikin kwato makaman, kana kuma ya yaba wa kwazon jami’an nasa da suke aiki tukuru ba dare ba rana wajen wanzar da tsaro a fadin jihar ya ce rundunar tasa ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba wajen yin maganin duk wani bata gari.