Rundunar ’yan sandan Najeriya ta tabbatar da kashe jami’anta 17 a harin Yobe
Dakarun sojin Najeriya da dama sun rasa rayukan a yayin da suke daƙile harin.
Rundunar ’yan sandan Najeriya ta tabbatar da kashe jami’anta 17 a wani harin da ’yan ta’adda suka kai wa wani sansanin horar da dakarun soji na musamman da ke Jihar Yobe.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DCP Anthony Okon Placid, ya fitar ranar Asabar ta ce an kashe jami’an ne ranar 8 ga watan Mayu.
- WHO ta ayyana ɓarkewar Ebola a Congo a matsayin barazanar lafiya ta duniya
- ’Yan takarar Gwamnan Yobe 3 a APC sun nace dole a yi zaɓen fid-da-gwani
“Rundunar ‘yan sandan Najeriya tana baƙin cikin sanar da kashe jami’anta 17 yayin da suke aikin bauta wa ƙasa sakamakon harin ta’addanci a Makarantar Dakarun Soji na Musamman da ke Buni Yadi a Ƙaramar Hukumar Gujba ta Jihar Yobe da sanyin safiyar 8 ga Mayun 2026,” in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa ‘yan sandan, waɗanda suke je makarantar domin samun horo na musamman, sun rasa rayukansu ne lokacin da ‘yan ta’adda suka kai jerin hare-hare a makarantar.
Sanarwar ta ce: “Kazalika jajirtattun dakarun sojin Najeriya da dama sun rasa rayukan a yayin da suke daƙile harin.”
Babban Sufeton ‘yansandan Nijeriya Olatunji Disu ya bayyana ‘yan sandan da aka kashe a matsayin waɗanda suke da “ƙarfin gwiwa da sadaukarwa” da nuna kishin ƙasa a yayin da suka halarci horo kan yaƙi da ta’addanci da wanzar da tsaro.
Ya miƙa saƙon ta’aziyyar ɗaukacin rundunar ‘yansandan Nijeriya ga iyalan jami’an da aka kashe tare da tabbatar musu cewa “ba za a taɓa mantawa da sadaukarwarsu ba.”
A wannan harin ta’addanci, jami’an tsaron Najeriya sun samu nasarar kashe mahara 50.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa, an kashe mayaƙa masu iƙirarin jihadi a lokacin da sojoji suka daƙile wani harin da ƙungiyar ISWAP ta kai a hedikwatar runduna ta 27 a garin Buni Gari da kuma wurin binciken ababen hawa na garin, wanda ke Jihar Yobe.